Sunaye: Za a yi Gagarumin Ruwan Sama na Tsawon Kwanaki 4 a Jihohi 6, NiMet

Sunaye: Za a yi Gagarumin Ruwan Sama na Tsawon Kwanaki 4 a Jihohi 6, NiMet

  • Hukumar hasashen yanayi ta NiMet ta sanar da cewa za a yi gagarumin ruwan sama a jihohin arewa 6 a cikin kwanaki hudu
  • Kamar yadda ta bayyana, jihohin Kaduna, Niger, Bauchi, Filato, Nasarawa da babban birnin tarayya ne zasu fuskanci ruwan mai yawa
  • Akwai jihohi da zasu fuskanci matsakaicin ruwa kamar Katsina, Zamfara, Kano, Kwara da sauransu amma zai taho da matsananciyar iska

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Hukumar hasashen yanain ta NiMet a hasashen yanayin da tayi na cikin kwanakin nan, ta hararo cewa za a yi ruwan sama mai matukar yawa a jihohi biyar na arewacin Najeriya tare da babban birnin tarayya.

Jihohin da gagarumin ruwan saman zai shafa sun hada da wasu sassan jihar Kaduna, Niger, Bauchi, Filato, Nasarawa da babban birnin tarayya, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan Kasuwa Sun Tafka Asara Yayin da Ruwan Sama Ya Mamaye Kasuwar Kantin Kwari

NiMets
Sunayen Jihohi: Za a yi Gagarumin Ruwan Sama na Tsawon Kwanaki 4, NiMet. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A rahoton yanayi na kwanakin nan, NiMet tace za a samu matsakaicin ruwan sama a jihohi kamar Kwara, Oyo, Kogi, Ogun, Ekiti, Ondo, Sokoto, Katsina, Zamfara, Kebbi, Kano, Jigawa, Yobe, Borno, Gombe, Adamawa, Taraba, Benue, Cross River, Akwa Ibom, Ebonyi, Enugu, Abia, Imo, Anambra, Rivers, Edo da Delta.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, ana tsammanin za a samu ruwan sama mara yawa suka matsakaici a wasu sassan kasar nan cikin kwanakin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Yayin da za a samu kadan ko kuma babu ruwan saman a wasu tsirarun jihohi. A sakamakon ruwan mai yawa a wasu jihohin, za a iya samun ambaliyar ruwa a tituna, rafuna da gidajen dake kwari.
"Hakazalika, ana tsammanin matsakaicin ruwan saman zai taho da iska mai karfi ballantana a jihohin arewacin Najeriya da tsakiyar kasar a cikin kwanakin.

Kara karanta wannan

Tsawa Ta Halaka Ango A Yayin Daukar Hotunan Kafin Aure Tare Da Amaryarsa

"Don haka ana shawartar jama'a da su kiyayi kwari , kada a yi tukin cikin ruwa, hanyoyin ruwa, a gujewa kasan bishiyoyi da duk wani wurin da bashi da tabbas a yayin ruwan kuma a kashe kayayyakin wutar lantarki kafin a fara ruwan saman," ya kara da cewa.

Kano: 'Yan Kasuwa Sun Tafka Asara Yayin da Ruwan Sama Ya Mamaye Kasuwar Kantin Kwari

A wani labari na daban, masu sana'ar sutturu a fitacciyar kasuwar Kantin Kwari suna cigaba da kirga asara bayan gagarumar ambaliyar ruwa ta lalata kayan sama da N200 miliyan a sama da shaguna 250 da rumfuna.

Wannan ya faru ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a ranakun Lahadi da Litinin a kusan dukkan yankunan birnin Kano wanda ya kawo ambaliyar ruwa har a ofishin hukumar taimakon gaggawa ta jihar, SEMA.

An kwashe sama da sa'o'i hudu ana zabga ruwan sama a kwaryar birnin a ranar Litinin, Daily Trust ta lura cewa manyan tituna da wasu anguwanni duk sun cika makil da ruwa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Hukumar DSS Ta Saki Fitacciyar Mai Goyon Bayan Ƙungiyar 'Yan Ta'adda a Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel