Bayan Kama Matashi da Sata a Kano, Masu Kaya Sun Fadi Sharadin Yafe Masa

Bayan Kama Matashi da Sata a Kano, Masu Kaya Sun Fadi Sharadin Yafe Masa

  • Jami'an bijilanti sun tarfa wani matashi dan asalin Katsina bayan zargin da ake yi masa na kutsa wa gidan mutane
  • Ana zargin matashin mai shekaru 20 da satar kayan abinci, wayoyin hannu da karafa wanda tuni ya sayar da su
  • Mutanen da ya shiga gidajensu sun bayyana cewa za a yafe masa, amma akwai babban sharadin da zai cika tukun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - An kama wani matashi, Mujahid Idris dan asalin jihar Katsina mai shekara 20 da ake zargi da shiga gidajen wasu mutane a jihar Kano ya na satar abinci.

Kara karanta wannan

Ahmad Isa: Mai gabatar da shirin Rai Dangin Goro a gidajen rediyo ya kwanta dama

Jami'an kungiyar tsaron sa kai da aka fi sani da bijilanti ne su ka yi ram da matashin bayan nemansa ruwa a jallo

Jihar
Mazauna Kano sun yafe wa matashin da ya masu sata Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ana zargin matashin da haura wa gidajen mutane a Mariri Gadon Arewa da ke karamar hukumar Kumbotso.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutanen da ya shiga gidajensu tare da yin satar sun amince da yafe masa, amma da sharadin ba zai sake zama a jihar Kano ba.

Ana zargin matashi da satar abinci

Jami'an sa kai ba kungiyar bijilanti sun bayyana kama matashin mai suna Mujahid Idris bayan an yi masa tara-tara bisa zargin satar kayan abinci.

Kwamandan bijilanti na karamar hukumar Kumbotso, Sani Abdullahi ya ce sun dade su na farautar matashin, amma sai yanzu aka yi nasarar kama shi.

Abubawan da ake zargin matashin ya sace

Kara karanta wannan

Matasa sun shuna wa yan sanda manyan karnuka, magana ta shiga kotu

Kwamandan bijilanti ya lissafa wasu daga cikin kayan da ake zargin Mujahid da sace da suka hada da kayan abinci da kayan karafa da yace tuni ya sayar da su.

Sauran abubuwan da ya amsa cewa ya sata sun hada da wayoyin Android da kudade, wanda tuni ya batar da su.

Kishi: Ana zargin ba yaro guba a Kano

A wani labarin kun ji cewa an kama wata mata, tare da gurfanar da ita a gaban kotu kan zargin kashe karamin yaro mai shekara daya tal da haihuwa.

Barista Abdussalam Dan Maidaki Sale wanda ya gabatar wa kotu tuhumar ya kafa hujja da cewa laifin ya sabawa dokoki da kundin tsarin mulki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.