NIMET ta yi hasashen cewa mamakon ruwan sama zai hana jirage tashi

NIMET ta yi hasashen cewa mamakon ruwan sama zai hana jirage tashi

  • Hukumar NIMET ta ce za ayi fama da mamakon ruwan sama mai karfi a wasu sassa na kasar
  • Ta ce za a iya samun ruwan sama mai yawa a jihohin Bauchi, Jigawa, Kano, Katsina, Zamfara, Kaduna, Kebbi, Sokoto da kuma Neja
  • Ana kuma sa ran samun ruwan sama matsakaici a jihohin Yobe, Kwara, Ogun, Osun, Ondo, Legas, Edo, Delta, Taraba,da Adamawa

Rahoton Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NIMET) ya yi hasashen samun mamakon ruwan sama a wasu yankunan kasa daga ranar Talata har zuwa Alhamis, jaridar Aminya ta ruwaito.

A wani jawabi na hasashen yanayi da NIMET ta saki a ranar Litinin, 6 ga watan Satumba, ta bayyana cewa akwai yiwuwar samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihohin Jigawa, Kaduna, Bauchi, Neja, Zamfara, Katsina da kuma Sokoto.

Kara karanta wannan

An shiga halin fargaba yayin da cutar Kwalara ta kashe mutane 25 a Ogun

NIMET ta yi hasashen cewa mamakon ruwan sama zai hana jirage tashi
NIMET ta yi hasashen cewa mamakon ruwan sama zai hana jirage tashi Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Rahoton ya kuma ruwaito cewa ana sanya ran samun ruwan sama matsakaici a jihohin Yobe, Kwara, Ogun, Osun, Ondo, Legas, Edo, Delta, Taraba, Adamawa daga ranar Talata, zuwa Alhamis.

Sauran su ne jihohin Ekiti, Filato, Nasarawa da Binuwai, Enugu, Ebonyi, Anambra, Abiya, Imo, Kuros Riba da Akwa Ibom.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har ila yau, ta ce akwai yiwuwar samun ambaliyar ruwa musamman a jihohin da ake sa ran samun mamakon ruwan, hakan kuma ka iya haifar da karyewar gadoji, rushewar gidaje da kuma hana tashin jirage.

Ta ce:

“Don haka, an shawarci jama’a da su yi taka-tsantsan, su guji wuraren da ba su da kasa da ruwa mai gudana.”

Hukumar ta kuma shawarci jama’a da su kasance cikin shiri don gujewa lahani daga hadarin da ke tattare da ruwan saman.

Sashin Hausa na BBC ta kawo cewa Shugaban na NIMET, Farfesa Mansur Baƙo Matazu, ya ce ana samun wannan yanayi ne sakamakon sauye-sauye na damuna wanda dama yawanci a farkon damina ruwan na zuwa babu karfi, sannan sannu a hankali zuwa karshen damina ruwa na karuwa.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifin Shugaban karama hukumar a jihar Bayelsa

Ruwa zai yi gyara: Masana sun ce za a iya barkewa da ambaliya a Jihohi 34 na tsawon kwana 3

A gefe guda, a baya mun kawo cewa, hukumar NIMET mai kula da yanayin gari ta yi gargadi cewa akwai yiwuwar a samu ambaliya a wasu jihohi 34 da ke Najeriya kwanan nan.

Da ta ke magana a ranar Talata, 23 ga watan Agusta, 2021, hukumar ta NIMET ta ce hakan na iya faru wa nan da kwana uku a cikin makon da ake ciki.

Matsakaita da ruwa mai nauyin da ake yi a halin yanzu za su iya kai ga samun ambaliya mai mugun karfi daga ranar Talata, zuwa Laraba, har Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel