Fitacciyar 'Yar TikTok a Arewa Ta Yi Bidiyo Tsirara, Hisbah Kano Ta Dauki Mataki

Fitacciyar 'Yar TikTok a Arewa Ta Yi Bidiyo Tsirara, Hisbah Kano Ta Dauki Mataki

  • Wata matashiyar 'yar TikTok, Hafsat Babu (baby) ta shiga bakin duniya bayan bidiyon tsiraicinta ya yadu a soshiyal midiya
  • A safiyar ranar Litinin, Kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Daurawa ya sanar da cewa sun kamo Hafsat bayan ganin aika-aikar da ta yi
  • A wani sakon murya da ba a kai ga tabbatarwa ba, 'yar TikTok din ta fito ta ce shekaru biyu da suka wuce ta dauki bidiyon bayan ta fito wanka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da cewa ta kama wata matashiyar ’yar TikTok, Hafsat Babu, wadda aka fi sani da Hafsat Baby kan laifin yin bidiyon tsirara.

Kara karanta wannan

Edo 2024: INEC ta gargadi Gwamna Obaseki, ta koka da halin yan siyasa

A karshen makon da ya gabata ne kafofin sada zumunta suka cika da maganganu kan bidiyon tsiraicin Hafsat Baby da ya yadu, lamarin da wasu ke ganin ya yi muni.

Hisbah ta cafke 'yar TikTok da ta yi bidiyo tsirara
Kano: 'Yar TikTok da ta yi bidiyo tsirara ta shiga hannun hukumar Hisbah. Hoto: mutan_kannywood
Asali: Instagram

Hisbah ta kama 'yar TikTok

Babban kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya sanar da kama Hafsat Baby tare da wallafa bidiyonta a ofishin hukumar inji rahoton Aminiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A safiyar Litinin Sheikh Daurawa ya fitar da bidiyon matashiyar a cikin wasu mata da hukumar ta kama, sai dai bai yi wani karin haske game da kamen ba.

Hafsat Babu ta shiga hannun Hisbah bayan an samu wani ya fitar da bidiyonta da ta dauka tsirara na kusan mintuna uku wanda ya jawo ce-ce-ku-ce.

'Yar TikTok ta yi tuban mazuru?

Idan ba a manta ba, a kwanakin baya hukumar Hisbah ta cafke Hafsat tare da wani matashi da suke yin bidiyo tare, inda suka yi rantsuwa cewa sun tuba daga yada tsiraici.

Kara karanta wannan

Rundunar tsaro ta fadi halin da Turji ke ciki bayan kisan Sabubu, ta sha alwashi

A wata hira da aka yi da Hafsat, ta ce ta tuba kuma ta goge dukkanin wani bidiyo da ya sabawa shari'a daga shafinta na TikTok.

Sai ga shi kwatsam an wayi gari da wannan sabon bidiyo na 'yar TikTok din, wanda duniya ta ganta tsirara haihuwar uwarta tana wasa da al'aurarta.

Bidiyon tsiraici: 'Yar TikTok ta magantu

Amma dai matashiyar, ta fito ta bayyana cewa wannan bidiyon ya fi shekaru biyu da ta dauke shi kuma ba ta san wanda ya fitar da shi ba yayin da ta ke cewa ita ba karuwa ba ce.

Sai dai Legit Hausa ba ta tabbatar da sahihancin muryar Hafsat da ke yawo na martani kan bidiyon tsiraicin ba, amma dai anji ta na cewa ta fito ne daga wanka ta dauki kanta a Snapchat.

Matashin da suke yin bidiyo tare da aka fi sani da Rabiu Lawancy, ya fito ya kare kansa kan bidiyon tsiraicin Hafsat, inda ya ce bai da masaniya kan rayuwar matashiyar.

Kara karanta wannan

"Na san komai": Tinubu ya magantu game da halin kunci, ya fadi silar shan wahala

A bidiyon da Dokin Karfe TV ta wallafa, Lawancy ya yi ikirarin cewa daukar bidiyo ne kawai ya hada shi da Hafsat kuma tun bayan nasihar da Hisbah ta yi masu ya daina yin aiki da ita.

Hisbah ta cafke Ramlat Princess

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar Hisbah ta Kano ta kama shahararriyar 'yar TikTok, Ramlat Princess kan zargin tallata madigo a shafinta na TikTok.

A kwanakin baya ne Ramlat Princess, wacce ta shahara wajen wallafa abubuwan da suka saba al'ada da nuna rashin tsoro ta wallafa wani bidiyo da ke tallata madigo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.