Ahmad Isa: Mai Gabatar da Shirin Rai Dangin Goro a Gidajen Rediyo Ya Kwanta Dama
- Mun samu rahoton cewa Allah ya yiwa fitaccen dan jaridar Najeriya da ke gabatar da shirin Rai Dangin Goro, Ahmad Isa rasuwa
- An rahoto cewa Ahmad Isa Koko wanda dan asalin jihar Kebbi ne ya rasu a birnin Legas bayan ya yi fama da rashin lafiya
- Legit Hausa ta samu jin ta bakin wasu masu sauraron shirin Rai Dangin Goro wadanda suka yi ta'aziyya tare da yiwa Ahmad addu'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Rahotanni sun bayyana cewa Allah ya karbi rayuwar shahararren mai gabatar da shirin 'Rai Dangin Goro,' Ahmad Isa Koko.
Wasu makusantan marigayin sun bayyana cewa fitaccen mai karanta littattafan adabin Hausa a gidajen rediyon ya rasu ne a birnin Legas.
Ahmad Isa Koto ya kwanta dama
Fitaccen dan jaridar da ya kware a nishadantar da masu saurare ta hanyar sarrafa muryarsa wajen karanta litattafai ya rasu bayan doguwar rashin lafiya, inji rahoton BBC Hausa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marigayi ahmad Isa Koko ya kasance ma'aikaci ne a gidan rediyon muryar Najeriya wanda aka fi sani da VON.
An ruwaito cewa marigayin wanda dan asalin karamar hukumar Koko Besse ne da ke jihar Kebbi, ya rasu yana da shekaru 61.
Tasirin shirin 'Rai Dangin Goro'
Zai yi matukar wahala ka samu wani matashi a Arewacin Najeriya, musamman ma a jihar Kano da zai ce bai san muryar Ahmad ba, muddin yana sauraron rediyo.
Shirinsa na 'Rai Dangin Goro' na daga cikin manyan shirye-shiryen rediyo da suka yi shuhura kuma suka samu miliyoyin masu sauraro musamman ma mata.
Marigayi Ahmad yana amfani da kwarewarsa da kuma fasahar da Allah ya ba shi ta sarrafa harshe wajen karanta littattafai wanda ke jan hankalin miliyoyin mutane.
Masu sauraro sun yi ta'aziyya
Legit Hausa ta samu jin ta bakin wasu daga cikin wadanda ke bibiyar karatuttukan marigayi Ahmad Isa Koko inda suka yi ta'aziyyar wannan babban rashi.
Sadiya Haruna Rijiyar Zaki, ta ce ta taso ne tana sauraron karatun littattan Hausa daga marigayin kuma shi ne ya sanya mata kwadayin adabin Hausa.
Sadiya ta ce kwana biyu da ba ta sauraron littattafan da ya ke karantawa ta daina sauraron gidajen rediyon kwata kwata, inda ta roki Allah ya gafarta masa.
Ita ma Hajiya Maina Ma'aji da ke Hayin Dan Kade a Kano, ta nuna alhini kan rasuwar dan jaridar, wanda ta ce shi ke debe mata kewa idan ta na ayyukan gida.
Hajiya Maina ta yi nuni da cewa salo da sarrafa harshen mamacin suka sa ya kerewa dukkanin masu karanta littattafai a gidajen rediyon Kano.
Marubuciyar addini ta rasu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Allah ya karbi rayuwar marubuciyyar littattafan addinin Musulunci kuma wadda ta kafa kungiyar FOMWAN, Aisha Lemu.
An ce Aisha Lemu ta rasu tana da shekaru 79.
Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Isa Pantami ya tabbatar da rasuwarta inda ya yiwa marigayiyar addua'ar Allah ya gafarta mata.
Asali: Legit.ng