Tinubu Ya Fasa Halartar Taron Majalisar Dinkin Duniya, An Bayyana Dalilin Zama a Gida

Tinubu Ya Fasa Halartar Taron Majalisar Dinkin Duniya, An Bayyana Dalilin Zama a Gida

  • Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ba zai samu damar halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) na bana ba
  • Fadar shugaban kasa ta sanar da cewa Tinubu ya fasa halartar taron da za a gudanar a New York saboda matsalolin da ke gida
  • A halin yanzu, Tinubu ya wakilta mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron UNGA

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Fadar shugaban kasa ta ce Shugaba Bola Tinubu ba zai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 za a gudanar a birnin New York ba.

Don haka shugaban ya umarci mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron UNGA na wannan shekarar.

Kara karanta wannan

Wahalhalu sun tsananta a Najeriya, Abdulsalami ya ba Tinubu muhimmiyar shawara

Shugaba Bola Tinubu ba zai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya na bana ba
Tinubu ya wakilta Shettima ya halarci taron majalisar Dinkin Duniya da za a gudanar a New York. Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Tinubu ba zai je taron UNGA ba

Mataimaki na musamman ga shugaban kasa Bola Tinubu a kan kafafen sada zumunta, Olusegun Dada ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar hadimin shugaban kasar ta ce:

"Bayan tafiye-tafiyensa zuwa kasashen China da Birtaniya, shugaban kasar ba zai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya na bana ba.
"A yanzu ya na son mayar da hankali kan al'amuran cikin gida da magance wasu kalubalen da kasar ke fuskanta, musamman bayan ambaliyar ruwa a wasu sassan kasar."

UNGA: Tinubu ya wakilta Shettima

A taron Majalisar Dinkin Duniya na 79, mataimakin shugaban kasa, Shettima zai gabatar da jawabin kasar Najeriya ga babban taron, a cewar sanarwar Dada.

Sanarwar ta kuma kara da cewa Shettima zai halacci wasu muhimman tarurruka da za a gudanar a gefen taron UNGA da kuma tattaunawa da shugabannin wasu kasashe.

Kara karanta wannan

Awanni bayan dawowarsa daga China, Tinubu ya yi muhimmin nadi a ofishin Ribadu

An rahoto cewa babban taron Majalisar Dinkin Duniyar zai gudana ne daga ranar Talata, 24 ga Satumba har zuwa ranar Asabar 28 ga watan.

UNGA 79: An rage tawagar Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya ce mutanen da za su wakilci Najeriya a taron Majalisar Dinkin Duniya na 2024 ba za su kai yawan na 2023 ba.

Shugaba Tinubu ya gargadi jami’an gwamnati da shugabannin hukumomi wadanda ba su da wani abu da za su yi a wajen taron da kada su halarta domin rage kashe kudin jama'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.