Shugaba Buhari ya yi albishir a taron UNGA, yace rashin tsaro yana shirin zama tarihi a Najeriya

Shugaba Buhari ya yi albishir a taron UNGA, yace rashin tsaro yana shirin zama tarihi a Najeriya

  • Muhammadu Buhari yace matsalar rashin tsaro ya kusa zuwa karshe
  • Shugaban Najeriyar ya bayyana haka wajen taron UNGA a New York
  • Najeriya ta saye wasu jiragen yaki daga hannun gwamnatin Amurka

USA - Shugaba Muhammadu Buhari yace matsalar rashin tsaron da ya addabi Najeriya ya kusa zuwa karshe domin kayan aiki sun kusa shigo wa hannu.

Mai girma Muhammadu Buhari yace jiragen Super Tucano da wasu jiragen yaki masu saukar ungulu da gwamnatinsa ta saya daga Amurka suna hanya.

Daily Trust tace shugaban Najeriyan ya yi wannan bayani a ranar Juma’a, 24 ga watan Satumbba, 2021, yayin da ake ta yin taro na majalisar dinkin Duniya.

Buhari ya shaida wa jakadar Amurka a majalisar dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield, cewa gwamnatinsa tana kokarin shawo kan matsalar rashin tsaro.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da Shugaba Buhari ya fada a jawabin da yayi a majalisar dinkin duniya

Ko Amurka ta taimaka wa Najeriya?

Shugaban kasar yace Amurka ta taimaka sosai wajen yakar ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga a Najeriya.

Shugaba Buhari ya yi albishir a taron UNGA, yace rashin tsaro yana shirin zama tarihi a Najeriya
Shugaba Buhari a UNGA Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

A wani jawabi da ya fitar ta bakin hadiminsa, Femi Adesina, shugaba Buhari yace gudumuwar Amurka ta ba sojoji da gwamnatin Najeriya kwarin-gwiwa.

Abin da ya canza salon yakin, ya kawo wa mutanen Najeriya zaman lafiya shi ne samun jiragen yaki da sojoji sama suke amfani da su wajen lallasa miyagu.

Ya Najeriya tayi fama da COVID-19?

Jaridar ta rahoto Buhari yana bayanin yadda gwamnatin tarayya tayi kokari wajen yakar sabon samfurin COVID-19 da yake kashe mutane a wasu kasashen.

“Mun samar da tawaga ta musamman ta kwararru da masana tare da hadin-kan jihohi, kuma muna tabuka abin kwarai idan aka duba adadinmu.”

Kara karanta wannan

Cikin jahilci muka yiwa yan Najeriya alkawarin canji, yanzu mun fahimci Jonathan na da gaskiya: Jigon APC

Buhari yace COVID-19 ba ta bambance wa tsakanin karami da babba ko kasa mai arziki da mara hali, don haka dole a tashi-tsaye domin a yaki kwayar cutar.

Kyau a yafe mana bashi - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya roki manyan kasashe 20 da ake da su a Duniya, suyi wa kasashe masu taso wa afuwar bashin da ake bin su.

An rahoto cewa Muhammadu Buhari yana so a ji tausayin kasashen da suke fama da rashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel