Awanni bayan Dawowarsa daga China, Tinubu Ya Yi Muhimmin Nadi a Ofishin Ribadu

Awanni bayan Dawowarsa daga China, Tinubu Ya Yi Muhimmin Nadi a Ofishin Ribadu

  • Rahotanni sun bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya sake yin wani sabon nadi awanni bayan dawowarsa daga kasar Sin da Birtaniya
  • Tinubu ya nada Ojukaye Flag Amachree a matsayin daraktan tsaron makamashi a ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro
  • Mai magana da yawun ofishin, Zakari Mijinyawa, ya ce nadin Amachree ya nuna himmar da Tinubu ya yi na karfafa tsaron makamashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Shugaba Bola Tinubu ya nada Hon. Ojukaye Flag Amachree a matsayin sabon daraktan tsaron makamashi a ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro (ONSA).

An ce nadin na Ojukaye Amachree wani bangare ne na kudirin gwamnati na tabbatar da samar da daidaito, dorewa, da samar da makamashi ga daukacin ‘yan Najeriya.

Kara karanta wannan

'Ka da mu zargi kowa': Tinubu ya bayyana abin da ya jawo ambaliyar Maiduguri

Shugaba Bola Tinubu ya yi muhimmin nadi a ofishin Nuhu Ribadu
Shugaba Bola Tinubu ya nada Amachree daraktan tsaron makamashi. hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Shugaba Bola Tinubu ya yi nadin mukami

Shugaban sashen sadarwa na ONSA, Zakari Mijinyawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 17 ga watan Satumba, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mijinyawa ya ce nadin Amachree ya kuma kara jaddada kudurin shugaba Tinubu na karfafa tsaro da makamashi yayin da ya ke magance matsalolin samar da makamashin.

Amachree ya na da digiri a fannin gudanarwa kuma tsohon dalibi ne a Makarantar Kasuwancin Legas.

Abin sani a kan Ojukaye Amachree

Jaridar Daily Trust ta rahoto Amachree ya shafe sama da shekaru 20 yana aiki bangaren harkokin kasuwanci, siyasa da kuma cudanya da bangaren makamashi.

Haka zalika, an ce ya na da kwarewa a fannin shugabanci na bangarorin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu musamman a yankin Neja Delta.

Kara karanta wannan

Karin farashin mai: Tsohon hadimin shugaba Jonathan ya soki al'umma, ya kare Tinubu

Sabon sashen ya na aiki ne kan daidaita manufofi, dabarun kariyar ababen more rayuwa, sarrafa bayanai, daidaitawar tsaro, ba da shawara kan haɗari a fannin makamashi.

Bola Tinubu ya dura Maiduguri

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya dura Maiduguri, babban birnin jihar Borno domin duba barnar da ambaliyar ruwa ta yi.

Rahoto ya nuna cewa Shugaba Tinubu ya ziyarci jihar Borno ne awanni bayan dawowarsa Najeriya daga wata ziyarar aiki a da ya kai kasashen UAE, China da Burtaniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel