Karin Farashin Mai: Tsohon Hadimin Shugaba Jonathan Ya Soki Al'umma, Ya Kare Tinubu

Karin Farashin Mai: Tsohon Hadimin Shugaba Jonathan Ya Soki Al'umma, Ya Kare Tinubu

  • Reno Omokri ya caccaki masu sukar Shugaba Bola Tinubu kan matakin NNPCL na kara farashin mai a Najeriya
  • Omokri ya ce mutane da dama ba su fahimci yadda ake gudanar da gwamnati ba shiyasa suke sukar Tinubu
  • Ya ce kamfanin duk da yana karkashin gwamnatin akwai manyan daraktoci da ke gudanar da lamuransa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya yi magana kan matakin NNPCL game da farashin mai.

Ya ce ya kamata a bar ganin laifin Bola Tinubu kan matakin da kamfanin NNPCL ya dauka.

Reno Omokri ya kare Tinubu kan karin farashin mai
Reno Omokri ya caccaki mutane da ke sukar Bola Tinubu kan karin farashin mai. Hoto: Reno Omokri, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Omokri ya magantu kan karin farashin mai

Omokri ya bayyana haka ne a shafinsa na X a jiya Laraba 11 ga watan Satumbar 2024.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Gwamna Zulum ya yi bayanin halin da ake ciki, ya faɗi kuɗin da Tinubu ya turo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon hadimin ya ce ya ce kuskure ne a zargi shugaban saboda NNPCL ya kara kudin mai.

Ya ce NNPCL mallakin Gwamnatin Tarayya ne amma akwai manyan daraktocin da ke kula da shi wanda su ya kamata a zarga.

"Rashin sani ne da fahimtar yadda ake gudanar da gwamnati yan siyasa da yan gwagwarmaya suna sukar Tinubu kan matakin da NNPCL ya dauka."
"NNPCL kamar CBN ne kuma mallakin Gwamnatin Tarayya wanda Tinubu ke da ikon naɗa shugabasu amma suna da yancin gudanar da ayyuansu."

- Reno Omokri

Omokri ya fadi ikon kamfanin NNPCL

Reno Omokri ya ce Gwamnatin Tarayya tana da kaso mai tsoka a hannun jarin kamfanin wanda ya ba ta damar nada shugaba.

Amma kuma kamfanin yana da ikon gudanar da lamuransa ba tare da katsalandan daga gwamnatin ba.

Kara karanta wannan

SERAP: An ba Tinubu wa'adin awa 48 ya janye karin kudin fetur, ya binciki NNPCL

Omokri ya ba yan Najeriya shawara

Kun ji cewa tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su rika siyan kayayyaki da ake samarwa a gida.

Omokri ya yi kiran ne yayin da ya kara jaddada cewa Naira ta tsaya a kasa da N1300 kan kowacce dala a kan farashin canji.

Daga nan ne ya bayyana wasu kayayyaki da kamfanonin da ya kamata 'yan Najeriya su koma amfani da su sosai a kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.