Mazauna Abuja Sun Shiga Tashin Hankali yayin da Aka Samu Karamar Girgizar Kasa
- An samu girgizar kasa tare da kara a wasu unguwanni da ke cikin kwaryar birnin tarayya Abuja na tsawon kwanaki uku a jere
- Rahotanni sun bayyana cewa mazauna yankin Mpape, P.W Neighbourhood da barikin Mopol 24 sun fuskanci wannan girgizar kasar
- Wannan girgizar dai ba ita ce karon farko da aka taba samu a yankunan Abuja ba, ko a shekarar 2018 sai da FEMA ta gargadi mutane
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa wasu unguwanni da ke cikin kwaryar birnin tarayya Abuja sun fuskanci wata karamar girgizar kasa ta kwanaki uku.
An ce mazauna yankin Mpape da ke karamar hukumar Bwari sun shiga cikin tashin hankali bayan girgizar kasar ta afku a wasu sassan garin.
An yi girgizar kasa a Abuja
Mpape na da tazarar tafiyar mintuna 10 daga babbar unguwar Maitama ta Abuja. Jaridar Daily Trust ta ce matsakaitan masu tattalin arziki ne suka mamaye unguwar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mazauna yankin sun bayyana cewa sun fara ganin girgizar kasar tare da wata kara a ranar Asabar kuma ta ci gaba a ranar Lahadi da kuma jiya, Litinin.
Jaridar The Guardian ta rahoto cewa girgizar kasar ta kuma afku a yankuna kamar P.W Neighbourhood da barikin Mopol 24.
An kuma ji karar girgizar kasar a kusa da mahadar Katampe, unguwar da ta hade da babbar hanyar Murtala Muhammad.
Mazauna Abuja sun firgita
Wani mazaunin unguwar, Obinna Ngozi ya ce gine-gine na girgiza a duk lokacin da kasar ta motsa, lamarin da ya haifar da fargaba a zukatan mutane.
Mazaunin ya ce ya ga girgizar kusan sau 10 a ranar Asabar daga lokacin da ta fara da misalin karfe 4 na yamma, ya kara da cewa lamarin ya kara ta’azzara washegarin ranar Lahadi.
Wani mazaunin anguwar, Muhammad Ibrahim, ya ce tun da farko sun yi tunanin ko tashin bam ne, domin a cewarsa, sautin ya sha bamban da na hakar ma'adinai.
Girgizar kasar Abuja a 2018
A shekarar 2018, Legit Hausa ta rahoto cewa an samu girgizar kasa marar karfi a yankin Mpape da Maitana da ke babban birnin tarayya Abuja.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta birnin tarayya (FEMA) ta fitar da wata takardar tabbatar da samun rahoton afkuwar girgizar kasar tare da daukar mataki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng