Yanzu yanzu: Gwamnati ta karyata jita jitar girgizar kasa a Abuja, ta bukaci jama'a su kwantar da hankulansu

Yanzu yanzu: Gwamnati ta karyata jita jitar girgizar kasa a Abuja, ta bukaci jama'a su kwantar da hankulansu

- Gwamnati ta fitar da rahoton yiyuwar afkuwar girgizar kasa a birnin tarayya Abuja

- Hukumar kula da agajin gaggawa ta birnin tarayya Abuja FEMA, ta bukaci mazauna birnin da su kwantar da hankulansu bisa rahoton girgizar kasa a wasu sassa na birnin

- A cewar hukumar, girgizar kasar na iya samun nasaba gajiyawar duwatsun karkashin kasa sakamakon yawan hakar ma'adai da ake yi a yankunan

Hukumar kula da agajin gaggawa na birnin tarayya Abuja FEMA, ta fitar da rahoton cewa dukkan alamu na girgizar kasa sun bayyana a Nigeria, biyo bayan rahotannin girgizar kasa da aka samu a wasu sassa na babban birnin tarayya Abuja.

Sai dai hukumar ta ce duk da alamun girgizar kasar, hakan ba wai yana nufin za'a samu ruftawar kasa a birnin tarayyar ba, don haka ta bukaci mazauna birnin dama daukacin yan Nigeria, da su kwantar da hankulansu.

Hukumar ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, 6 ga watan Satumba, inda ta ce girgizar kasar na iya afkuwa ta dalilin gajiyawar duwatsun karkashin kasa sakamakon yawan hakar ma'adai da ake yi a yankunan.

Sanarwar ta kuma ce girgizar kasar na iya samun nasaba da fitar sinadarai daga ma'adanan kasa, wadanda ke haddasa ragargajewar duwatsu, daga karshe su samar da nakasu ga karfin duwatsun na zama a waje daya, wanda hakan zai tilasta girgizar kasar.

KARANTA WANNAN: 2019: Kudirin Saraki na tsayawa takarar shugaban kasa, kamar almara ne - APC

Da dumi dumi: Akwai alamun za'ayi girgizar kasa a birnin tarayya Abuja - FEMA
Da dumi dumi: Akwai alamun za'ayi girgizar kasa a birnin tarayya Abuja - FEMA
Asali: Facebook

Har ila yau, sanarwar ta bayyana yadda wasu mazauna yankunan Maitama, Jabi, Utako, Gwarimpa da kuma Mpape da sauransu suka kai rahoton jin motsin kasa a yankunan.

Wasu mazauna Jabi da suka zanta da Legit.ng sun ce sau biyu suna jin kasar na girgiza a ranar Talata, 4 ga watan Satumba, wacceta ci gaba da faruwa tun daga wancan lokaci har zuwa yanzu.

Daya daga cikin mazauna yankin Jabi, Jerrywright Ukwu, ya ce: "Muna iya jin girgizar kasa, hakan ya faru ba sau daya ba, ta na girgiza gidaje da karfin gaske, musamman a jiya (Alhamis). A cire batun wasa, akwai bukatar hukuma ta duba wannan lamarin cikin gaggawa. Girgizar na faruwa ne da karfin gaske, ina fatan dai hakan ba zai haifar da ruftawar kasar ba"

Haka zalika, da yawa daga cikin mazauna yankunan sun bayyana faruwar hakan, musamman ma shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki, da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, dukansu sun bayyana faruwar hakan a shafukansu na Twitter.

Sai dai a cikin sanarwar, hukumar kula da agajin gaggawa ta birnin tarayya Abuja FEMA, ta bukaci mazauna birnin da su kwantar da hankulansu bisa rahoton girgizar kasa a wasu sassa na birnin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel