Yanzu Yanzu: An sake samun girgizan kasa a Abuja
- Al'umman yankin Mpape sun shiga halin dar-dar kan zargin afkuwar girgizar kasa a yankin
- An tattaro cewa wata majiya tayi ikirarin cewa lamarin yayi sanadiyar mutuwar mutane uku
- Amma mataimakin daraktan sasin kula da kasa na NGSA, Abba Usman, yace kara da motsin da ya afku a Mpape ya kasance sakamakon sakamakon cire wani abun fashewa da ya lalace ba bisa ka'ida ba
Rahotanni sun kawo cewa an sake samun girgizar kasa a Mpape, wani yanki da ke Abuja a ranar Juma’a, 8 ga watan Maris.
Sai dai akwai wani ikirari da ba a tabbatar ba wanda yace girgizan kasar yayi sanadiyar mutuwar mutane uku.
Mazauna yankin sun bayyana cewa girgizar kasar ya afku ne da misalin karfe 2:00 na tsakar dare lokacin da mafi akasarinsu ke bacci.
Lamarin ya shafi gine-gine da dama a yankin. Wata da ke zama a yankin mai suna Favour ta tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Thisday. Tace lamarin yayi sanadiyar mutuwar mutane uku a garin.
Tace ta wayi gari ta ga dakinta cike da kura kuma abubuwa da dama sun tarwase a wajen.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan iska sun cinna ma ofishin INEC wuta a Akwa Ibom
A ranar 8 ga watan Satumban shekarar da ya gabata ne yankin Mpape suka fuskanci girgizar kasa lamarin da ya sanya tsoro a zukatan mutane da dama.
Da yake martani akan laarin, mataimakin daraktan sasin kula da kasa na NGSA, Abba Usman, yace kara da motsin da ya afku a Mpape ya kasance sakamakon cire wani abun fashewa da ya lalace ba bisa ka'ida ba.
Usman yace kamfanin ta nemi izini daga ma'naikatar ma'adinai da karafuna don ta cire sinadaran da ta sanya saboda ta daina aiki.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng