Kwamitin Shugaban Kasa ya bayyana abinda ya haddasa Girgizar 'Kasa a garin Abuja

Kwamitin Shugaban Kasa ya bayyana abinda ya haddasa Girgizar 'Kasa a garin Abuja

Mun samu rahoton cewa, kwamitin da fadar shugaban kasa ta kafa domin gudanar da bincike kan 'yar takaitacciyar girgizar kasa da ta auku cikin garin Abuja a tsakanin ranakun 5 zuwa 8 ga watan Satumba, ya bayyana sakamakonsa.

Kwamitin ya bayyana cewa, yawaitar haƙa rijiyoyin burtsatsai da kuma yasar ruwa a kullum ita ta haddasa 'yar taƙaitacciyar girgizar kasar ta auku a babban birnin kasar nan na tarayya.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, kwamitin ya kuma bayyana cewa akwai yiwuwar girgizar kasar za ta ci gaba da aukuwa a kasar nan muddin ba a kawo ƙarshen zaizaiyar kasa da ke aukuwa a sakamakon haƙa rijiyoyin burtsatsai.

Cikin wani binciken ilimin kimiyya da fasaha da kwamitin ya gudanar ya tabbatar da cewa, akwai yiwuwa mai ƙarfin gaske ta ci gaba da aukuwar girgizar kasa cikin lokuta na gaba a fadin Najeriya.

Kwamitin Shugaban Kasa ya bayyana abinda ya haddasa Girgizar 'Kasa a garin Abuja
Kwamitin Shugaban Kasa ya bayyana abinda ya haddasa Girgizar 'Kasa a garin Abuja
Asali: Depositphotos

Farfesa Sa'idu Muhammad, jagoran kwamitin kuma shugaban cibiyar binciken kimiya ta kasa NASRDA (National Space Research Development Agency), shine ya bayyana hakan inda yace akwai rijiyoyin burtsatsai 110, 000 da aka haƙa cikin birnin Abuja kuma ake yasar kimanin tan 330, 000 na ruwa a kowace rana.

KARANTA KUMA: Atiku ya kere sauran 'yan takarar jam'iyyar PDP ta fuskar cancantar Shugabanci

A yayin haka kuma, Ministan kimiya da fasaha na Najeriya, Dakta Ogbonnaya Onu, ya bayar da tabbacin cewa kwamitin zai ƙara kaimi wajen ci gaba da gudanar da bincike kan wannan annoba da ba a saba da ita ba a kasar nan.

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnatin tarayya ta daura damarar gudanar da bincike tare da kawo hanyoyin daƙile da kuma tsare-tsaren riga kafi kan aukuwar girgiza a lokuta na gaba cikin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: