"Dan Adamawa ne": Matashi Ya Yi Layar Zana Bayan Ya Sace Motar Hukumar EFCC

"Dan Adamawa ne": Matashi Ya Yi Layar Zana Bayan Ya Sace Motar Hukumar EFCC

  • A wani al’amari mai ban mamaki, hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta fara farautar wani matashi da ake zargi da satar motarta
  • Hukumar ta ayyana wanda ake zargin, Ibrahim Mohammed mai shekaru 26 da haihuwa, a matsayin wanda ta ke nema ruwa a jallo
  • Yanzu haka dai hukumomi na neman jama’a da su taimaka wajen gano wannan matashi, wanda aka ce mazaunin jihar Adamawa ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A ranar Juma'a ne hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta ayyana Ibrahim Mohammed, mai shekaru 26 a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.

EFCC na farautar Ibrahim Mohammed ne bisa zargin satar wata mota mallakin hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawar.

Kara karanta wannan

Labarin Husaina: Hedikwata ta yi magana kan zargin Janar da zalunci, an dauki mataki

Matashi ya tafkawa EFCC sata, an ayyana nemansa ruwa a jallo bayan satar mota.
Wani matashi ya tsere bayan ya sace motar EFCC, an fara nemansa ruwa a jallo. Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

Matashi ya saci motar hukumar EFCC

An sanar da fara neman matashin ne a cikin wata sanarwa daga kakakin EFCC, Dele Oyewale da aka wallafa a shafin hukumar na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dele Oyewale, ya bayyana cewa ana zargin Mohammed, dan asalin karamar hukumar Jada a jihar Adamawa da sace motar hukumar EFCC.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Ana sanar da jama’a cewa hukumar EFCC na neman Ibrahim Mohammed bisa zargin sata da kuma mallakar motar EFCC ba bisa ka’ida ba."

EFCC ta yi kira ga duk wanda ke da labarin inda Mohammed yake da ya yi magana, inda ta bukaci jama’a da su tuntubi ofisoshin hukumar da ke a fadin kasar.

EFCC na farautar matashi

Hukumar ta EFCC ta samar da hanyoyi da dama domin ba da rahoton inda matashin ya ke, ciki har da layin waya da adireshin imel, wanda ke nuna muhimmancin lamarin.

Kara karanta wannan

Ambaliyar Maiduguri: Mutanen da aka ceto daga gidaje sun haura 3,600

Adireshin Mohammed na ƙarshe shi ne 56, titin Japa Bariki, jihar Adamawa.

Hukumar EFCC ta nemi taimakon jama’a domin gano shi, ta kuma umurci masu masaniya da su tuntubi ofisoshinta da ke manyan garuruwan da suka hada da Ibadan, Legas, da Abuja.

Ana sa ran hukumar EFCC za ta kara zage damtse wajen kwato motar da aka sace tare da kamo wanda ake zargin.

EFCC na neman matashi kan N935m

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar EFCC ta fara farautar Adewale Joyeoba, wanda ya ke aiki a kamfanin Wales Kingdom Capital bisa zargin damfara.

EFCC ta ce tuni ta kama kama Emmanuel da Victoria Jayeoba, wadanda su ne iyayen Adewale bisa zargin su da hannu a damfarar naira miliyan 935.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.