EFCC na neman wani mutum ruwa a jallo, ta saki hotonsa ga duk wanda ya gan shi
- Wani mazaunin Lagas, Emmanuel Elegbenosa, na wasan yar tsere da hukumar EFCC
- Hukumar yaki da rashawar na zargin mutumin da aikata zamba
- Masu damfara ta yanar gizo da dama sun shiga hannun hukumar a yan kwanakin nan
Hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta nemi taimakon 'yan Najeriya wajen gano wani da ake zargi wanda ake zargi da damfara.
Hukumar a shafinta na Twitter a ranar Asabar, 13 ga watan Fabrairu, ta kaddamar da neman mutumin mai suna Emmanuel Elegbenosa, ruwa a jallo.
EFCC ta bayyana cewa ana binciken mai laifin ne kan laifuka da suka shafi yanar gizo.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya nada wani sabon shugaban tsaro
Hukumar ta bayyana cewa adireshin wanda ake zargin mai shekaru 28 na karshe da aka sani shine yankin Elegushi da ke jihar Lagas.
Wallafar da EFCC ta yi ya janyo martani masu ban dariya daga wajen wasu yan Najeriya.
Karanta wasu daga cikin martanin a kasa:
Isah Harun @ IsahHarun1 ya ce:
'Wai daman mikiya na nan da ranta.''
KU KARANTA KUMA: FG ta ce ma’aikatan jami’a sun yarda da janye yajin aiki, ta yi karin haske kan bude jami’o’i a fadin kasar
DAGUX @AvuvakarAmeenu ya ce:
“Don Allah EFCC nima ku wallafa hotona.”
Kay @ Kelvin413 ya ce:
''Nawa za ku biya?”
bjay @ Bolaji2512 ya ce:
''Jami'an Gwamnati nawa kuka hukunta saboda aikata rashawa a kujerar mulki. An kafa hukumar ku ne don yaki da cin hanci da rashawa a cibiyoyin gwamnati amma kun karkata zuwa bin jama'a sama da kasa. ''
J.K EBaDS #NNM @ ebads007 ya ce:
''Ba za mu taimaka muku wajen neman kowa ba. mahimman mutanen da ya kamata ku fuskanta suna tafiya hankalinsu kwance a cikin Aso Rock. Ku je can ku yi aikinku!"
A wani labarin, yayinda ake tsaka da fargaba sakamakon kama masu zanga-zangar #OccupyLekkiTollGate da aka yi a ranar Asabar, 13 ga watan Fabrairu, an dan samu nutsuwa na dan lokaci bayan motar yan sandan ya tsaya cak.
Motar yan sandan wanda a kan yi amfani da shi wajen daukar fursunoni, shine aka yi amfani da shi waen kama masu zanga-zangar, Channels TV ta ruwaito.
A cewar kafar watsa labaran, sai da jami’an kamfanin Lekki Concession Company (LCC) suka tura motar.
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng