EFCC na neman matashi mai shekaru 24 ruwa a jallo bisa tafka damfarar N935m

EFCC na neman matashi mai shekaru 24 ruwa a jallo bisa tafka damfarar N935m

  • Hukumar EFCC ta bayyana cewa tana neman wani Adewale Daniel Jayeoba ido ruwa-a-jallo
  • Tana neman sa ne sakamakon damfarar N935m da ya tafka tare da hadin guiwar iyayen sa
  • Tun watan Yuni iyayen sa suka zo hannun hukumar, amma an neme shi sama ko kasa an rasa

Jihar Osun - Hukumar yaki da rashawa da harkokin yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta na neman wani Adewale Joyeoba, wanda yake aiki karkashin Wales Kingdom Capital Limited, bisa zargin sa da tafka damfara.

Kamar yadda The Cable ta ruwaito, hukumar ta bayyana sanarwar ne a ranar Litinin.

EFCC na neman matashi mai shekaru 24 ruwa a jallo bisa tafka damfarar N935m
Adewale Jayeoba da EFCC ke nema ruwa a jallo. Hoto: The Guardian
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

EFCC ta kama 'yan damfara ta intanet 30 a jami'ar KWASU

Sanarwar da hukumar ta fitar ya ce:

“Ana sanar da jama’a cewa hukumar EFCC ta na neman Adewale Daniel Jayeoba na Wales Kingdom Capital sakamakon zargin sa da hannu a wata damfara.
“Jayeoba dan shekara 24 ne kuma dan asalin karamar hukumar Ori-Ade ne da ke karkashin jihar Osun.”
“Adireshin sa da aka sani na karshe shi ne 1004, Providence Centre, titin MKO Abiola kusa da gidan man NNPC a Abeokuta, jihar Ogun.”

A watan Yuni, EFCC ta ce jami’an ta daga ofishin ta na jihar Legas su ka kama Emmanuel da Victoria Jayeoba, wadanda su ne iyayen yaron mai shekaru 24 da ake nema bisa zargin su da damfarar naira miliyan 935.

Kamar yadda EFCC ta bayyana:

“Wadanda aka kama sun hada kai ne da dan su wanda har yanzu ake neman sa yana aiki da wani Ponzi Scheme ne da sunan ya na kasuwanci inda yake yasar kudaden al’umma."

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana dalilin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan kudirin Tinubu

Bincike ya gano cewa mahaifin sa ne shugaban kamfanin da suke damfarar

The Cable ta kara ruwaito yadda bincike ya gano cewa Emmanuel wanda shi ne darektan Wales Kingdom Capital inda ya ke aiki da asusun bankuna 5 kuma ya shigar da N18,397,913.67 kafin a kama shi.

“Da aka tsananta bincike, an gano cewa Victoria wacce ta bude asusun bankuna 6 ta yashi kudin jama’a har N916,607,715.48.”

Hukumar EFCC ta bukaci duk wanda ya samu labari akan matashin ya yi gaggawar sanar da ko wanne ofishin ta dake fadin kasar nan.

Hotunan mutumin da aka kama ya damfari mutane 64 miliyoyin naira a Kano

A wani rahoton daban, Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani hatsabibin dan damfara bisa zargin sa da amfani da sunan babban bankin Najeriya wurin yasar dukiyar mutane 64 ta hanyar amfani da takardun bogi, LIB ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Cafke Sajan Ɗan Sanda Da Harsasai 370 a Plateau

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Laraba, 8 ga watan Satumba inda yace an kama wanda ake zargin, Buhari Hassan a Yankaba Quarters ne da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel