Kotu Ta Sake Zama kan Zargin Tsohon Minista a Kebbi da Dirkawa Budurwa Ciki

Kotu Ta Sake Zama kan Zargin Tsohon Minista a Kebbi da Dirkawa Budurwa Ciki

  • Kotu a Kado da ke Abuja ta yi zama kan zargin tsohon Minista a Najeriya da dirkawa wata budurwa ciki
  • Ana zargin Kabiru Tanimu da yaudarar wata mai suna Hadiza na tsawon shekaru wanda har ta samu sami juna biyu
  • Sai dai Ministan ya musanta dukan zarge-zargen da Uwani da yarta, Hadiza ke yi masa inda ya ce su suka yaudare shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - An gurfanar da tsohon Ministan ayyuka na musamman, Kabiru Tanimu kan zargin yi wa wata ciki a Abuja.

Kotun da ke Kado a Abuja ta dakatar da yan sanda daga cigaba da tuhumar tsohon Ministan a gwamnatin Goodluck Jonathan.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru, Gwamna Abba ya sakawa yarinyar da taimaka masa a zaben 2019

Kotu ta dakatar da yan sanda kan cigaba da tuhumar tsohon Minista
Kotu ta dage sauraran karar da aka shigar da tsohon Minista. Hoto: Kabiru Tanimu Turaki.
Asali: Facebook

Alkali ya hana korafi daga wadanda ke kara

Premium Times ta ce alkalin kotun, Shehu Ahmadu ya gargadi Musa Baffa da Uwani Arabi da yarsu, Hadiza Baffa kara korafi saboda matsalar na gaban kotu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan zargin Kabiru Tanimu da yi wa wata Hadiza ciki tare samun haihuwa wanda ya musanta hakan.

Tanimu ya ce a 2016 ya hadu da uwani inda ta ke neman taimako da shawarinsa kan yarta, Hadiza.

Tsohon Ministan ya ce ya taimaka musu da kudi rijista a Jami'ar Baze har N1m daga cikin N3m inda Uwani ta bukace shi da ya zama mai kula da harkokin yarta.

Har ila yau, Turaki ya ce ya cigaba da daukar wasu bukatunta ashe bai sani ba sun haɗa baki inda suka sauya sunan babanta zuwa na shi.

Daga nan ne ya kore su, bayan wata biyu Uwani ta sake kiransa inda ta ce masa yarta, Hadiza na dauke da ciki kuma shi ne ubansa wanda ya musanta tun farko.

Kara karanta wannan

"Ba zan sake mara maka baya a siyasa ba": Ministan Tinubu ga yaronsa gwamnan PDP

Wandanda ke kara sun ƙaryata tsohon Minista

Sai dai a ɓangarensu, Uwani da yarta, Hadiza sun musanta dukkan abin da Turaki ya fada game da abin da ya faru tun farko.

Suka ce Turaki ne ya fara sauya sunan babanta zuwa na shi lokacin da ya saya mata mota wanda ya yi ta yaudarta tare da kwanciya da ita har ta samu juna biyu.

Hadiza ta ce ta sha barazana daga Turaki lokacin da ta fada masa tana da ciki inda ya bukaci a zubar da shi amma ta ki.

Ta ce daga bisani ta haifi jaririn a watan Afrilun 2024 wanda har ya dauki nauyin dawainiyarsa a asibiti.

Daga nan Alkalin kotun ya dage cigaba da sauraran karar zuwa ranar 24 ga watan Satumbar 2024.

An zargi Kabiru Turaki da karkatar da kudi

Kun ji cewa ana zargin tsohon Minista, Kabiru Tanimu Turaki da ya rike mukamin a lokacin mulkin Goodluck Jonathan da badakalar kudi.

Kabiru Turaki wanda ya nemi takarar shugaba kasa a 2015 ya taba rike Ministan kwadago, kuma ya na cikin jagororin jam'iyyar PDP a fadin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.