"Tinubu Ya Sani": Bayan Kisan Halilu Sabubu, Gwamnatin Zamfara Ta Jefa Babban Zargi

"Tinubu Ya Sani": Bayan Kisan Halilu Sabubu, Gwamnatin Zamfara Ta Jefa Babban Zargi

  • Ana tsaka da murnar kashe dan ta'adda, Halilu Sabubu, gwamnatin Zamfara ta magantu kan batun rashin tsaro
  • Kakakin gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Idris ya ce akwai makarkashiya a lamarin tsaron jihar kowa ya sani
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake zargin juna tsakanin gwamnatin Zamfara da kuma ta Bello Matawalle da ta shude

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - Kakakin gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Idris ya yi magana kan rashin tsaro.

Idris ya ce shugaban kasa ya san duk maso kawo tsaiko kan rashin zaman lafiyar da ake fama da shi.

Gwamnatin Zamfara ta yi magana kan makarkashiya a harkar tsaron jihar
Gwamnatin Zamfara ta zargi wasu da hannu a lamarin rashin tsaron jihar. Hoto: Dauda Lawal Dare.
Asali: Facebook

Gwamnatin Zamfara ta magantu kan rashin tsaro

Kara karanta wannan

'Akwai ƙarancin abinci:' Zulum ya fadi halin da ake ciki kwanaki 3 da ambaliya

Mai magana da yawun gwamnan ya fadi haka a bidiyon YouTube da Channel TV ta wallafa a yau Juma'a 13 ga watan Satumbar 2024.

Idris ya ce abin da ke faruwa a jihar Zamfara kowa ya sani makarkashiya ce da wasu ke yi.

Kakakin gwamnan ya koka kan yadda aka mayar da rashin tsaron siyasa domin ba ta sunan Gwamna Dauda Lawal.

Ya ce akwai wasu manyan mutane a sama da suke kawo tsaiko kan lamarin kuma shugaban kasa ya sansu.

Zamfara ta na zargin ana siyasantar da rashin tsaro

"Akwai masu siyasantar da rashin tsaron jihar Zamfara, shugaban kasa ya sansu, kowa ya sansu."
"Suna yin haka ne saboda su bata sunan gwamnatin jihar Zamfara saboda wasu bukatunsu na siyasa."
"Ba zan kira suna ba amma ba su son kawo karshen rashin tsaro saboda su cigaba da zargin gwamnatin jihar domin sun ga ya kawo cigaba fiye da na su."

Kara karanta wannan

Karin farashin mai: Tsohon hadimin shugaba Jonathan ya soki al'umma, ya kare Tinubu

- Sulaiman Idris

Idris ya ce daga kaga wasikar da aka fitar kan zargin Dauda Lawal kowa ya sani akwai makarkashiya a cikin lamarin tsaron jihar Zamfara.

An kashe Halilu Sabubu a Zamfara

A wani labarin, kun ji cewa rundunar sojoji ta hallaka kasurgumin dan bindiga, Halilu Sabubu a jihar Zamfara.

Sojojin sun hallaka Sabubu ne kwana biyu bayan fitar da bidiyo yana kira ga sauran yan ta'adda a yankin.

A bidiyon, Sabubu ya bukaci a takaita kai wa al'umma hare-hare tare da mayar da hankali kan jami'an tsaro kawai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.