Mazauna Kano Sun Tashi da Takaici, An Tsinci Jaririya a ƙarkashin Tayar Mota

Mazauna Kano Sun Tashi da Takaici, An Tsinci Jaririya a ƙarkashin Tayar Mota

  • Mazauna 'Yar Akwa da ke yankin Na'ibawa a karamar hukumar Tarauni sun wayi gari da tsintsar jaririya da wasu su ka jefar
  • An tsinci jaririyar ne a karkashin tayar mota, inda aka yi fargabar karnuka ko wani mugun abu zai iya samunta
  • Mai unguwar 'Yar Akwa, Malam Jamilu Abba Danladi ya tabbatar da cewa yanzu haka jaririyar ta na hannunsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Mai unguwar ‘yar Akwa, Jamilu Abba Danladi, ya bayyana takaicin yadda aka jefar da jaririya a karkashin tayar mota a Na’ibawa da ke karamar hukumar Tarauni a jihar Kano.

Kara karanta wannan

An samu asarar rai bayan gini ya sake rikitowa a Kano

Mai unguwar ya bayyana cewa a daren Lahadi ne aka zo har gida a sanar da shi cewa an ga wata jaririya, inda su ka garzaya wajen.

kano map
An tsinci gawar jarirya a Kano Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mai unguwar ya shiga takaicin lamarin, amma ya tabbatar da cewa yanzu haka ya karbo jaririyar.

Yadda aka tsinci jaririya a Kano

Daya daga cikin wadanda su ka je ganin jaririyar bayan an tsince ta, Shamsuddeen Sabi'u ya ce su na zaune wajen teburin mai shayi aka zo masu da labarin jin kukan jaririya.

Shamsuddeen ya ce da farko sun yi zaton ko kukan mage aka jiwo, amma da su ka karasa sai su ka ga ashe jaririya aka jefar.

Kano: Mai unguwa ya shawarci jama'a

Mai unguwar ‘yar Akwa, Jamilu Abba Danladi, ya shawarci jama'a a kan su rika sanya idanu kan mata masu goyo ko dauke da wani abu da za a gani su na yawo.

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke budurwar wani rikakken ɗan bindiga a Taraba, bayanai sun fito

Ya bayyana cewa ta haka ne za a iya gaggawar kiran hukuma idan an lura da wani motsi na rashin gaskiya, inda ya shawarci matan da su ji tsoron Allah SWT.

Daliba ta jefar da jaririyarta

A wani labarin kun ji yadda abin takaici ya afku a jami'ar tarayya ta Dutse (FUD), inda wata jaririya ta haifi diyarta mace amma ta kashe ta ta hanyar jefo ta daga saman bene.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan Jigawa, DSP Shiisu Lawan Abdullahi ne ya tabbatar da afkuwar mummunan lamarin, inda ya ce ana zurfafa bincike a kai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.