Sojoji Sun Cafke Budurwar Rikakken Ɗan Bindiga a Taraba, Bayanai Sun Fito
- Rundunar soji ta 6 da ke a Jalingo, ta kama wata mata da ake zargin tana aikawa masu garkuwa da mutane ne bayanai a jihar Taraba
- Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Kyaftin Oni Olubodunde, ya ce ana zargin matar budurwa ce ga rikakken dan bindiga ‘Chen’
- Hakazalika, rundunar ta 6 ta kuma yi nasarar kwace wata mota da aka sameta dauke da bindiga AK47 da kuma katin shaida na NURTW
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Taraba - Rahotanni sun bayyana cewa sojojin Najeriya sun cafke wata mata da ake zargin tana aikawa masu garkuwa da mutane bayanai a jihar Taraba.
A cewar mukaddashin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta 6 a Jalingo, Kyaftin Oni Olubodunde, an kama wadda ake zargin ne a ranar 6 ga Satumba, 2024.
An cafke budurwar dan bindiga
Kyaftin Oni Olubodunde ya ba da sanarwar cewa sojojin sun kama matar ne a a kauyen Sondi da ke karamar hukumar Wukari a jihar, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce wadda ake zargin mai suna Miss Markus Grace budurwa ce ga wani fitaccen dan bindiga mai suna ‘Chen’ wanda aka ruwaito yana addabar mazauna yankin.
Kyaftin Oni ya ci gaba da cewa, a halin yanzu wadda ake zargin tana tsare kuma ana ci gaba da bincike domin gano zurfin da ta yi a taimakawa 'yan ta'addar.
Sojoji sun kama bindigar AK47
Kakakin rundunar ya kuma bayyana cewa sojojin sun kama wata mota kirar Toyota Yaris mai lamba Taraba KLD 652 XA dauke da bindiga kirar AK-47 da kuma wata gidan harsashin AK-47.
Ya ce sojojin rundunar ta 6 a lokacin da suke aikin sintiri a garin Bantaje da ke Wukari a ranar 5 ga Satumba, 2024, suka tare motar kuma direbanta ya tsere bayan ganin sojojin.
Kyaftin Oni ya ce a lokacin da aka gudanar da bincike kan motar, an kuma tsinci katin shaida na 'yan kungiyar NURTW mai dauke da sunayen Isa Ibrahim da Malam Isa Garin Tukura.
'Yan sanda sun kama 'yan kwarmato
A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar 'yan sandan Katsina ta ce ta samu nasarar cafke mutane hudu da ke tattara bayanan sirrin jama'a su na mikawa masu garkuwa da mutane.
Wani yaro mai shekaru 13, Umar Hassan na daga cikin mutane hudu da jami'an tsaron su ka cafke bisa zargin taimaka wa miyagun, inji sanarwar ASP Abubakar Sadiq.
Asali: Legit.ng