Da duminsa: Direba ya banke dan KAROTA, ya kara wa wandonsa iska

Da duminsa: Direba ya banke dan KAROTA, ya kara wa wandonsa iska

  • Wani direba wanda ba a san ko waye ba ya kade jami'in KAROTA a jihar Kano tare da tserewa kuma ba a kama shi ba
  • Kamar yadda aka tattaro, ya banke jami'in ne a titin jami'ar Bayero da ke tsakiyar birnin Kano kuma ya gudu
  • Kakakin hukumar KAROTA ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce an mika gawar asibitin Murtala

Wani direba da ba a san ko waye ba a jihar Kano ya banke tare da kashe jami'in hukumar kula da lamurran tituna, KAROTA da ke titin BUK a tsakiyar birnin Kano.

Daily Nigerian ta tattaro cewa, direban ya tsere bayan ya banke jami'in KAROTA kuma abokan aikinsa sun yi kokarin cafkarsa amma abun ya gagara.

Da duminsa: Direba ya banke dan KAROTA, ya kara wa wandonsa iska
Da duminsa: Direba ya banke dan KAROTA, ya kara wa wandonsa iska. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

A yayin da aka tuntubi mai magana da yawun KAROTA, Nabilusi Abubakar, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce an mika gawar jami'in asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan yari, sun saki fursunoni 240 sannan suka kashe sojoji a Kogi

Abubakar ya ce ba zai iya kara cewa komai ba game da lamarin saboda hukumar na jiran rahoton aukuwar lamarin ne daga asibitin, Daily Nigerian ta ruwaito.

Ya kara da daukan alkawarin samar da karin bayani bayan an kammala bincike.

Damfarar daukar aiki: An dakatar da mataimakin shugaban marasa rinjayen majalisar Nasarawa

A wani labari na daban, majalisar jihar Nasarawa ta dakatar da mataimakin shugaban marasa rinjaye, Luka Zhekaba wanda aka fi sani da PDP-Obi 2 kan zarginsa da ake da daukar aikin bogi na malamai 38 na makarantun sakandare a jihar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, kakakin majalisar, Ibrahim Abdullahi, ya sanar da wannan yayin zaman majalisar a ranar Litinin a Lafia.

Dakatar da Zhekaba ya zo ne bayan majalisar ta tattauna kan rahoton kwamitin ilimi na majalisar kan daukar aikin malamai 366 da wasu 38 na bogi da aka gani wurin jerin biyan kudin albashi na jihar.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jam'iyyar APC ta fatattaki tsohon gwamna da wasu mambobi 40

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng