Dada Yar’Adua Zuwa Hakimin Bichi: Yadda Aka Rasa Sarakai da Fitattu 6 a Awa 120
Abuja - A cikin kwanaki kalilan, fitattu da shahararrun mutane da yawa suka rasu a Najeriya daga karshen Agusta zuwa Satumba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Mun yi kokarin kawo wasu daga cikin wadanda Allah SWT ya yi wa rasuwa a kwanakin nan.
Manyan mutanen da aka rasa a mako
1. Habibah Shehu Idris
A ranar Juma’a, 30 ga watan Agusta 20 aka ji matar Sarkin Zazzau Shehu Idris ta rasu bayan ta yi fama da gajerar rashin lafiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An samu labarin mutuwar Hajiya Habibah Shehu Idris ne a shafin Zazzau_Emirate a X, ta kasance surukar Sarki Ahmad Bamalli.
2. Tanimu Zailani
A safiyar ranar Lahadi aka samu labarin cikawar Mai shari’a Tanimu Zailani kuma tuni aka yi masa sutura a Rigachikun a jihar Kaduna.
Zailani ya rike alkalin alkalan jihar Kaduna daga 2013 zuwa 2018. Marigayin yaya ne ga tsohon shugaban majalisa, Rt. Hon. Yusuf Zailani.
3. Bashir Banadeen
Cikin dare a ranar Lahadi Legit Hausa ta samu labarin mutuwar Alhaji Bashir Banadeen wanda ya cika bayan fama da rashin lafiya.
An sanar da cewa za a yi wa Bashir Banadeen sallar gawa a masallacin Marigayi Alhaji Haruna Danja da ke kusa da ABU Congo Zaria.
4. Garba Gashuwa
A watan nan ne kuma aka rasa Alhaji Garba Gashuwa wanda fitaccen mawakin siyasa ne a kasar Hausa, ya rasu ya kusa shekaru 70.
Mawakin ya shahara da wakar da ya yi wa shugaba Ibrahim Badamasi Babangida. Tuni dai aka birne shi a garin Kano inda yake zaune.
5. Dada Yar’adua
Ranar Litinin kuma sai ga labara maras dadi daga jihar Katsina, mahaifiyar tsohon shugaban Najeriya, Hajiya Dada Yar’adua ta rasu.
An birne Dada Yar’adua a Katsina kamar yadda aka birne ‘ya ‘yanta irinsu Janar Shehu Musa Yar’adua da Ummaru Musa Yar’adua.
6. Idris Bayero
Alhaji Idris Bayero yana cikin manyan mutanen da aka rasa a watan Satumban nan, shi ne ‘dan auta a cikin ‘ya ‘yan Sarki Abdullahi Bayero.
Ado Bayero ya fara nada shi Dan Darman Kano kuma hakimin Rimin Gado. Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi masa sallah a kofar Kudu.
Shugabannin DSS da aka yi a tarihi
Idan aka shiga wani babin, za a ji labari shugaban farko da aka yi a tarihin DSS shi ne Ismail Gwarzo da Ibrahim Babangida ya nada a 1986.
Bayan Kayode Are, Yusuf Magaji Bichi shi ne shugaban da ya fi kowa dadewa a hukumar DSS, Muhammadu Buhari ya nada shi a 2018.
Asali: Legit.ng