Rahoto: Yadda Aka Kashe Mutane 13,346 tare da Sace 9,207 a Mulkin Tinubu
- Wani rahoto na bayan bayan nan ya nuna cewa mutane 13,346 aka kashe yayin da aka sace mutane 9,207 a karkashin mulkin Bola Tinubu
- Rahoton ya ce daga ranar 29 ga watan Mayun 2023 zuwa Satumbar 2024 an samu karuwar tashe tashen hankula musamman a Arewacin kasar
- Masana dai na nuna damuwarsu kan kalubalen tsaro da aka gaza magancewa, suna kuma kira ga Shugaba Tinubu da ya dauki kwararan matakai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Tun bayan rantsar da Shugaba Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayun 2023, Najeriya ta fuskanci tashe-tashen hankula, inda aka kashe mutane 13,346 tare da sace 9,207 a fadin kasar.
An alakanta wadannan tashe tashen hankulan ga hare haren 'yan bindiga, 'yan fashi, rikicin manoma da makiyaya, da dai sauran nau'ikan tada zaune tsaye.
Jaridar The Punch ta ce wani tahoton tsaron Najeriya na baya-bayan nan daga Beacon Consulting, wani kamfani da ya kware kan harkokin tsaro, ya bayar da cikakken bayani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton kisa da satar mutane
Daga watan Mayu zuwa Disambar 2023, an sami rahoton kisan mutane 5,802 da kuma yin garkuwa da mutane 2,754.
Al’amarin ya kara ta’azzara a shekarar 2024, inda aka kashe mutane 7,544 tare da sace 6,453 tsakanin watan Janairu zuwa Satumba.
Masana dai na nuna damuwarsu kan kalubalen tsaro da aka gaza magancewa, suna kuma kira ga Shugaba Tinubu da ya dauki kwararan matakai.
A wani taro a watan Yuli, Shugaba Tinubu ya bayyana rashin tsaro da ake fama da shi a yankin Arewa maso Yamma a matsayin rashin tsaro da aka gada.
Dabarun magance rashin tsaro
Duk da haka, masanan sun yi ikirarin cewa ana buƙatar dabarun da suka dace domin magance rashin tsaron, inda har wani mai sharhi kan harkokin tsaro, Nnamdi Chive ya ba da shawarwari.
Nnamdi Chive ya jaddada cewa:
"Akwai bukatar a kula da iyakokin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma sosai domin hana wasu baki daga kasashen waje tada zaune tsaye a cikin kasar."
A nasa bangaren, kwararre kan harkokin tsaro, Kanar Yomi Dare, ya bayyana irin rawar da matsalar tattalin arziki da cin hanci da rashawa ke takawa wajen ta’azzara matsalar tsaro.
Lokacin kawo karshen ta'addanci
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta sha alwashin daukar dukkanin matakan da suka dace domin murkushe ta'addanci da 'yan ta'adda.
Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, wanda ya bayyana hakan ya ce gwamnonin jihohin da ke fama da rashin tsaro na aiki kafaɗa da kafaɗa datarayya domin kawo karshen lamarin.
Asali: Legit.ng