Kalubalen tsaro a Najeriya ya kusa zama tarihi, IGP ya jaddada

Kalubalen tsaro a Najeriya ya kusa zama tarihi, IGP ya jaddada

- Sabon sifeta janar na 'yan sanda Najeriya ya jaddada cewa matsalar tsaro ta kusa zuwa karshe a kasar nan

- Ya sanar da hakan ne yayin bikin yaye wasu jami'an 'yan sanda da suka samu horarwa a fanin shugabanci

- Ya ce hukumar 'yan sandan Najeriya na aiki da sauran hukumomin tsaro wurin shawo kan matsalar

Usman Baba, sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, ya ce jami'an tsaro na aiki tukuru wurin tabbatar da cewa sun shawo kan matsalar tsaron kasar nan, The Cable ta ruwaito.

Baba, wanda ya samu wakilcin DIG Danmallam Mohammed, ya sanar da hakan ne yayin da ake yayen 'yan sandan da suka samu horo a bangaren shugabanci a kwalejin 'yan sanda dake Jos.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito, ya ce hukumar 'yan sanda na aiki tukuru wurin dawo da zaman lafiya a dukkan sassan kasar nan kuma tana hada kai da sauran hukumomin tsaro.

"Muna aiki tukuru wurin tabbatar da zaman lafiya tare da daidaituwa ta dawo dukkan sassan Najeriya," yace.

KU KARANTA: Buhari zai yi bikin sallah a fadar Aso Rock, yace baya bukatar gaisuwar sallah

Kalubalen tsaro a Najeriya ya kusa zama tarihi, IGP ya jaddada
Kalubalen tsaro a Najeriya ya kusa zama tarihi, IGP ya jaddada. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: An sheke jami'an 'yan sanda 6 yayin da 'yan bindiga suka kai farmaki ofishin 'yan sanda

"Tsaro al'amari ne ya da shafi kowa, ba zamu iya yin shi mu kadai ba. Muna yin iyakar kokarinmu tare da hada kai da sauran hukumomin tsaro wurin tabbatar da tsaro.

"Da izinin Ubangiji tare da taimakon 'yan Najeriya, za mu shawo kan ta'addanci, 'yan bindiga, garkuwa da mutane da dukkan wani nau'i na rashin tsaro a kasar nan."

IGP ya sha alwashin horarwa za ta zama wani jigo na mulkinsa saboda hakan ne kawai zai tabbatar da ingancin tsaro a kasar nan.

A yayin nasiha ga wadanda suka samu horon, Baba ya kwatanta zanga-zangar EndSARS da abu mara dadi tare da kira ga jami'an da su sake duba hakkokin dan Adam yayin da zasu fara shugabanci.

A wani labari na daban, a cikin kwanakin karshen mako ne hankulan jama'a suka tashi a Hotoro ta arewa dake karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano bayan sojoji sun cafke wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne.

Samamen da sojin suka kai a daren Asabar sun dira wani sabon gida ne da aka gano cewa jama'an daga jihar Borno suka tare. Kamar yadda takardar da aka fitar ta bayyana, an tabbatar da kama mutum 13.

Tun a farkon zuwan Boko Haram jihar Kano, Hotoro ce cibiyar ayyukansu kafin a tarwatsa su sakamakon kokarin jami'an tsaro da na mazauna yankin, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel