NNPP Ta Samu Koma Baya a Kano: 'Yan TikTok din Kwankwasiyya Sun Sauya Sheka

NNPP Ta Samu Koma Baya a Kano: 'Yan TikTok din Kwankwasiyya Sun Sauya Sheka

  • Kungiyar 'yan TikTok din Kwankwasiyya sun hakura da tafiyar gidan Sanata Rabiu Kwankwaso inda suka koma gidan Sanata Barau Jibrin
  • A ranar Alhamis ne tawagar 'yan TikTok din suka ziyarci Sanata Barau tare da sanar masa da ficewarsu daga jam'iyyar NNPP zuwa APC
  • Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya nuna jin dadinsa da shigowarsu APC, inda ya kira su da 'Yan TikTok din Barau Jibrin Maliya'

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta sake rasa wasu daga cikin jiga jigan magoya bayanta, wadanda suka taka muhimmiyar rawa a lokacin yakin neman zabensa.

A ranar Alhamis, 5 ga watan Satumba, bisa jagorancin shugabanninsu, kungiyar 'yan TikTok din Kwankwasiyya suka sanar da ficewarsu daga tafiyar Abba Gida Gida.

Kara karanta wannan

Sanata Barau ya sake yiwa tafiyar Kwankwasiyya illa, jiga jigan NNPP sun koma APC

'Yan TikTok din Kwankwasiyya sun fice daga NNPP sun koma APC
Sanata Barau Jibrin ya karbi 'yan TikTok din Kwankwasiyya da suka sauya sheka zuwa APC. Hoto: @barauijibrin
Asali: Twitter

'Yan Kwankwasiyya sun koma APC

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ya sanar da hakan a shafinsa na X, yayin da ya wallafa hotunansa tare da 'yan TikTok din.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Barau ya bayyana cewa tawagar 'yan TikTok din sun koma jam'iyyar APC bisa jagorancin Sulaiman Umar Abdullahi (Memory), Ummawuyya Dalhat Sani da Saminat Abdullahi.

'Yan TikTok din da suka hada da maza da mata, sun ajiye jar hula da jajayen mayafai, inda suka ce sun dawo daga rakiyar jam'iyyar NNPP mai mulki a Kano, yanzu sun koma APC.

Sanata Barau ya karbi 'yan TikTok

Sanata Barau ya nuna tsantsar farin cikinsa da wannan mataki na matasan, inda ya ce daga yanzu za a rika kiransu da 'Yan TikTok din Barau Jibrin Maliya.'

A cewar mataimakin shugaban majalisar dattawan:

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya ta sake yin rashi: Fitaccen mawaki a Arewa ya fice daga NNPP zuwa APC

"Da wannan ci gaba ne matasan masu fada a ji da suka hada da maza da mata, a yanzu sun kuduri aniyar inganta ayyukan babbar jam’iyyarmu ta APC.
"Mataimakin sakataren kudi na jam'iyyarmu ta kasa Hon. Dattuwa Ali Kumo ya shaida dawowar 'yan TikTok din Kwankwasiyya."

An ce mai ba sanatan shawara ta kan harkokin mata, Hajiya Yardada Maikano Bichi ce ta canza jajayen mayafin matan 'yan TikTok din wanda ya nuna ficewarsu daga NNPP.

Jiga jigan NNPP sun koma APC

Tun da fari, mun rahoto cewa wasu jiga jigan NNPP a jihar Kano sun sauya sheka zuwa APC a ranar Alhamis, ciki har da shugaban 'yan kasuwar fetur da gas na jihar, Alhaji Hassan Nuhu.

Sanata Barau I. Jibrin ne ya karbi jiga jigan zuwa APC, inda ya yi masu maraba tare da ba su tabbacin cewa jam'iyyarsu za ta yi wa kowa adalci ba tare da bambanci ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.