Arewa Za Ta Samu Sauki: 'Yan Sanda Sun Cafke Masu Garkuwa da Mutane a Kaduna

Arewa Za Ta Samu Sauki: 'Yan Sanda Sun Cafke Masu Garkuwa da Mutane a Kaduna

  • Rundunar 'yan sandan Kaduna ta ce ta samu nasarar cafke mutane 11 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a sassan jihar
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ya ce an cafke mutane a karamar hukumar Lere kuma an kwato makamai
  • Haka zalika, an kwato makamai, kudi, kayan tsafi da sauransu bayan da aka kama wasu miyagun a lokuta daban daban a Satumba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Rundunar ‘yan sanda ta cafke wasu mutane 11 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar Kaduna da ke shiyyar Arewa maso Yamma.

A wasu ayyukan samame daban daban da 'yan sandan suka gudanar, sun cafke 'yan ta'addan tare da kwato makamai da sauran kayayyaki.

Kara karanta wannan

Ana zaman makokin kisan mutane 34, 'yan Boko Haram sun sake kai hari a Yobe

Rundunar 'yan sanda ta yi magana kan kama masu garkuwa da mutane a Kaduna
Kaduna: 'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 11 a Kaduna. Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ya fitar a ranar Alhamis, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kaduna: An cafke masu garkuwa 4

Sanarwar ta ce a tsakiyar watan Agusta, jami’an ‘yan sanda daga Saminaka tare da hadin gwiwar mafarauta sun kai samame a wasu kauyuka uku a karamar hukumar Lere.

Kauyukan su ne: Maraban Wasa, Gurzan Hakimi Mariri, da Abugan Kurama, inda aka kama mutane hudu da ake zargi da satar mutane.

Mutanen da aka cafke su ne: Abdulhamid Abubakar, Danjuma Luka, Ayuba Simon, da Idi Saleh.

Sanarwar ta ce abubuwan da aka kwato sun hada da wata karamar bindiga guda daya, koriyar mota kirar Golf, babur Bajaj da wayoyin hannu guda takwas.

An cafke mutum 7 a jihar Kaduna

Kara karanta wannan

Ana jimamin kashe mutane 87 a Yobe, 'yan bindiga sun sake kai hari a jihar Arewa

Jaridar The Nation ta rahoto ASP Mansir Hassan, ya kara da cewa:

"A ranar 2 ga Satumba 'yan sanda suka cafke wasu mutane shida bayan yi masu kofar rago a wata tashar mota. An kwato bindigogi, harsasai, kudi, kayan tsafi da dai sauransu.
"A ranar 3 ga Satumba, 'yan sanda sun rutsa wani Yahaya Yusuf a wani otel a Tafa, karamar hukumar Kagarko wanda bayan kama shi ya amsa laifin garkuwa da mutane da satar shanu."

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, ya bukaci jama’a da su ci gaba da ba ‘yan sanda hadin kai tare da bayar da tabbacin za a kara kaimi wajen yaki da miyagun ayyuka.

Masu garkuwa sun kashe malami a Kaduna

A wani labarin, mun ruwaito cewa masu garkuwa da mutane sun kashe shugaban makarantar Koriga da ke jihar Kaduna bayan da suka yi garkuwa da shi da matarsa mai juna biyu.

A zantawarsa da jaridar Legit, tsohon Sanata, Shehu Sani wanda ya ba da labarin kashe shugaban makarantar, ya nuna damuwa kan hare-haren 'yan bindiga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.