Shettima Ya Sa Labule da Minista, Ribadu, Kyari Yayin da Farashin Fetur Ya Kai N1200
- Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya dauki babban mataki kan yadda farashin fetur ya yi tashin gwauron zabi
- An ce daukar matakin ya rataya a wuyan Shettima ne kasancewar Shugaba Bola Tinubu ba ya kasar lokacin da aka kara kudin
- A matakin da ya dauka, mataimakin shugaban kasar ya gana da Nuhu Ribadu, Mele Kyari da Heineken Lokpobiri a Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya saka labule da karamin ministan man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri da shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari.
Haka kuma, Shettima ya gayyaci mai bai shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu zuwa taron da ke gudana a fadar shugaban kasa, ranar Alhamis.
Dalilin ganawar Shettima da su Ribadu
Rahoton Channels TV ya nuna cewa mataimakin shugaban kasar ya kira taron ne domin tattaunawa kan karin kudin fetur da NNPC ya yi a kwanan nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matakin da Shettima ya dauka na zuwa ne yayin da ake sayar da litar fetur kan N1,200 a wasu sassan kasar. An ce lamarin ya jawo zanga zanga a Kano, Yobe da Delta.
‘Yan Najeriya sun fuskanci karin farashin man fetur ba zato ba tsammani a ranar Talata, 3 ga watan Satumba. Farashin litar ya tashi daga kusan N600 zuwa N1,200.
Yadda aka kara kudin man fetur
Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, majiya mai tushe ta bayyana cewa kamfanin na NNPC Limited ya bayar da umarnin kara farashin mai.
A Legas, gidajen man NNPC sun tabbatar da karin farashin zuwa N855 kan kowace lita bayan amincewar hukumar kula da dillalan man fetur ta kasa NNPC.
Karin farashin na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan da kamfanin ya sanar da cewa yana fuskantar kalubale wajen shigo da mai saboda wani gagarumin bashi na dala biliyan shida.
Zanga zanga ta barke a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa masu sana'ar tuka adaidaita sahu a jihar Kano sun gudanar da zanga zangar adawa da kara kudin fetur da kamfanin NNPCL ya yi.
'Yan adaidaita sahun sun nuna takaicin yadda aka kara kudin a daidai wannan lokaci da 'yan kasar ke fama da matsin tattalin arziki, inda suka ce karin zai jawo tsadar rayuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng