"Ba Zamu Yarda Ba" Sabuwar Zanga-Zanga Ta Ɓarke a Jihar Arewa, Harkoki Sun Tsaya Cak Kan Abu 1

"Ba Zamu Yarda Ba" Sabuwar Zanga-Zanga Ta Ɓarke a Jihar Arewa, Harkoki Sun Tsaya Cak Kan Abu 1

  • Masu Adaidaita sahu sun fantsama kan tituna zanga-zanga kan matsin lambar jami'an YOROTA a Damaturu, babban birnin jihar Yobe
  • Ƴan Keke Napep sun bayyana cewa jami'an sun matsa musu da tarar maƙudan kuɗi kama daga N5,000 zuwa N20,000 kan laifin da bai taka kara ya karya ba
  • Sai dai shugaban ƙungiyar direbobin Keke Napep na Yobe ya ce ba shi da masaniyar wannan zanga-zanga da ake yi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Yobe - Mambobin ƙungiyar direbobin Keke Napep sun mamaye tituna suna zanga-zanga a Damaturu, babban birnin jihar Yobe da safiyar yau Talata.

Direbobin Napep watau adaidaita sahu sun hargitsa Damaturu ne kan abinda suka kira matsin lambar karɓan kuɗaɗe da hukumar sufurin jihar (YOROTA) ke musu.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ƴan bindiga suka halaka ƴan kasuwa kusan 10 a jihar Arewa

Yan adaidaita sahu sun fantsama kan tituna a Yobe.
Harkoki Sun Tsaya Cak a Yobe Yayin Masu Keke Napep Suka Fara Zanga-Zanga a Damaturu Hoto: Channelstv
Asali: UGC

A cewarsu, jami'an hukumar kula da sufurin jihar Yobe sun matsa musu lamba, kullum suna karɓan kuɗaɗe daga ƴan adaidaita sahu, kuma su ce kowa sai ya canza rijista.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zangar ta tsaida harkoki cak a Damaturu

Tuni dai zanga-zangar ta gurgunta harkokin tattalin arziki saboda an ga mutane da dama sun makale saboda babu motoci ko Napep ɗin da zata kai su zuwa wurin aiki.

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, wannan zanga-zanga ta shafi kananam yara ƴan makaranta domin ba su samu damar tafiya makarantunsu ba.

Meyasa ƴan Adaidaita sahu suka fara zanga-zanga?

Ƴan adaidaita sun bayyana cewa duk da halin da ake ciki na matsin tattalin arziki a ƙasar nan amma gwamnatin Yobe na ƙara jefa su cikin wahala.

Masu zanga-zangar sun ce jami'am YOROTA sun tsangwami direbobin Napep kuma sun matsa musu da tara kan laifin da bai taka kara ya karya ba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Amarya ta hallaka mijinta a jihar Neja

A rahoton Daily Trust, Bukar Adamu, wani mai Napep da ke cikin zanga-zangar ya ce:

"Suna cajin mu makudan kuɗaɗe daga N5,000 zuwa N20,000 kan ɗan ƙaramin laifi, mun gaji haka nan. Bara suka kirkiro wata tara ta N40,000 ko N20,000 suka tilasta mana biya."

Shugaban kungiyar masu Keke Napep na jihar, Umaru Barau ya shaida cewa zanga-zangar haramtacciya ce domin ba su da masaniya.

Ya kuma yi alƙawarin ba da lokaci domin zantawa da ƴan jarida bayan ya gana da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.

Gwamna Bago ya saki jagorar zanga-zanga

A wani rahoton na daban Gwamna Umar Bago na jihar Neja ya bada umarnin sakin jagorar waɗanda suka yi zanga-zanga a Minna, Aisha Jibrin, da wasu mutum 24

Kwamishinar yaɗa labarai da dabaru ta jihar, Binta Mamman, ta ce an ɗauki wannan mataki ne bayan dogon nazari kan abinda ya sa a kama su

Asali: Legit.ng

Online view pixel