“Al’umma Suna da Rawar da Za Su Taka”: Buhari Ya Magantu kan Matsalar Tsaro

“Al’umma Suna da Rawar da Za Su Taka”: Buhari Ya Magantu kan Matsalar Tsaro

  • Tsohon shugaban kasa ya tura sakon ta'aziyya ga Gwamna Mai Mala Buni na Yobe da kuma al'ummar jihar kan harin yan ta'adda
  • Buhari ya nuna damuwa kan harin inda ya yi musu addu'ar samun rahama tare da neman daukar mummunan mataki kan miyagun
  • Tsohon shugaban ya ce tabbas idan al'umma suka samu goyon bayan gwamnati za su taka muhimmiyar rawa wurin dakile rashin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi magana kan matsalar tsaro a Najeriya.

Buhari ya ce akwai rawar da al'umma za su taka kan matsalar tsaro musamman idan suka samu goyon bayan gwamnati.

Buhari ya jajantawa al'ummar Yobe kan harin ta'addanci
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nuna damuwa ta'addanci a Najeriya. Hoto: Muhammadu Buhari.
Asali: Getty Images

Muhammadu Buhari ya nuna damuwa kan ta'addanci

Kara karanta wannan

"Za mu bi maku hakkin ku," Tinubu ya sha alwashi kan kisan Bayin Allah a Yobe

Tsohon shugaban kasa ya fadi haka ne a shafinsa na Facebook inda ya jajantawa al'ummar jihar Yobe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari ya nuna damuwa kan farmakin da aka yi a jihar inda 'yan Boko Haram suka kai mummunan hari.

Buhari ya yi wa gwamna, mutanen Yobe ta'aziyya

Ya tura sakon jaje na musamman ga Gwamna Mai Mala Buni da sarakunan gargajiya da kuma al'ummar jihar Yobe gaba daya.

Har ila yau, Buhari ya kuma yi musu addu'ar samun rahama inda ya bukaci daukar tsattsauran mataki kan wadanda suka aikata laifin.

Daga bisani, Buhari ya yi addu'ar samun zaman lafiya da walwala da kuma cigaba a fadin Najeriya baki daya.

Yadda 'yan ta'adda suka hallaka mutane

Yayin harin a karamar hukumar Tarmuwa da ke jihar, mutane da dama sun rasa rayukansu a ranar Lahadi da ta gabata.

Kara karanta wannan

"A yi amfani da tsarin IBB": Janar Akilu ya ba Tinubu shawarar magance rashin tsaro

Miyagun yan ta'addan sun hallaka mutane tare da kona shaguna da gidaje a yayin harin.

Jana'izar Dada: Bashir Ahmad ya kare Buhari

Kun ji cewa tsohon hadimin Muhammadu Buhari ya yi magana kan rashin zuwan zuwansa jana'izar Hajiya Dada Yar'adua.

Ana yadawa a kafofin sadarwa cewa Buhari yana Daura amma bai halarci jana'izar mahaifiyar marigayi Umaru Musa Yar'Adua ba.

Bashir Ahmad ya fadi dalilin hakan a shafinsa na X a jiya Laraba 4 ga watan Satumbar 2024 domin cirewa mutane kokwanto.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.