An Shiga Tashin Hankali a Neja, 'Yan Ta'adda Na Shirin Korar Mutane daga Gidajensu

An Shiga Tashin Hankali a Neja, 'Yan Ta'adda Na Shirin Korar Mutane daga Gidajensu

  • Rahoto ya nuna 'yan daba sun umurci mazauna rukunin gidajen M.I Wushishi da ke Minna da su bar gidajensu ko dai a kashe su
  • An ce 'yan ta'addan wadanda ake zaton masu hakar ma'adainai ne sun farmaki rukunin gidajen tare da lalata motoci da gidaje
  • Rundunar 'yan sandan jihar Neja wadda ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce an kashe mutum daya a kokarin tarwatsa 'yan daban

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Wasu ‘yan ta'adda sun umurci mazauna rukunin gidajen M.I Wushishi da ke Minna, babban birnin jihar Neja da su fice daga gidajensu ko kuma a kashe su.

An ce ‘yan dabar sun kai farmaki rukunin gidajen a lokacin da mafi yawan mazajen unguwar suka tafi wajen aiki, inda suka rika lalata motoci da gidaje.

Kara karanta wannan

Gina gidaje 500 a Kano: Dan kwangila ya harzuka minista, an gindaya masa sharuda

"Yan sanda sun yi magana bayan 'yan daba sun farmaki rukunin gidaje a Neja
'Yan daba sun umarci mazauna wani rukunin gidaje a Neja da su fice daga gidajensu.
Asali: Original

'Yan daba sun farmaki gidaje

Wani mazaunin rukunin gidajen da ya zanta da jaridar Punch ya ce harin ya zo ne bayan da mazauna unguwar suka je kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda da ke unguwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mazaunin unguwar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

“Yan dabar da muke zargin masu hakar ma’adinai ne sun bukaci daukacin mazauna rukunin gidajen M.I Wushishi da ke Minna, jihar Neja da su bar gidajensu ko kuma a kashe su.
“Wadannan mutanen sun farmaki rukunin gidajen da tsakar rana, inda suka lalata motoci da kuma tagunan gidaje."

'Yan sanda sun yi magana

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun a ranar Talata, ya tabbatar da faruwar harin amma ya ce an samu zaman lafiya a yankin yanzu.

“A ranar 2 ga watan Satumba muka samu kiran gaggawa cewa wasu da ake zargin masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba sun kai farmaki a rukunin gidajen M.I Wushishi, Minna.

Kara karanta wannan

Gobara ta babbake rukunin gidajen ma'aikatan gwamnati, bayanai sun fito

“Tawagar ‘yan sanda karkashin DPO Maitumbi sun je wurin, inda aka tarwatsa ’yan ta’addan, amma an kashe mutum daya wanda ba a iya gano ko wanene ba zuwa yanzu."

Wasiu Abiodun ya ce yanzu dai an jibge jami'an tsaro a rukunin gidajen domin dakile duk wani farmaki da ka iya faruwa nan gaba, inji rahoton AIT.

'Yan fashi sun farmaki fadar Minna

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu da ake kyautata zaton cewa 'yan fashi ne sun kai farmaki fadar mai martaba Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago.

An ce Sarki Bahago na cikin fadarsa a lokacin da maharan suka bude wuta kan mai uwa da wabi, daga bisani suka yi awon gaba da makudan kuɗin da ba a san iyakarsu ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.