Yan ta'adda sun kaiwa wani dan takara mummunan hari tare da lalata motoci 21
- Yan ta'adda sun kaiwa wani dan takarar APC hari a garin Suleja, jihar Niger inda suka lalata motocin yakin zabensa 21
- An kai harin ne a wani gidan sayar da mai a ranar Litinin
- Ana zargin cewa magoya bayan dan majalisar wakilai ta tarayya a mazabar mai ci a yanzu ne suka dau nauyin harin
Wani dan takarar majalisar wakilai ta tarayya a mazabar Suleja/Tafa, jihar Niger, karkashin jam'iyyar APC, Ado Abubakar ya sha da kyar bayan da wasu 'yan ta'adda suka kai masa mummunan hari a garin Suleja ranar Litinin.
Ana zargin cewa 'yan ta'addan da suka kai harin a sha-tale-talen titin zuwa Kaduna a Suleja, sun aikata hakan ne da sa hannun magoya bayan Abubakar Lado, dan majalisar wakilai ta tarayya na mazabar mai ci a yanzu, wanda kuma ya ke neman tazarce a zaben 2019.
Banda Abubakar, 'yan ta'addan sun raunata wasu mutane 3, wadanda aka garzaya da su babban asibitin Umaru Musa Yar'adua da ke Sabo Wuse don yi masu magani. Daya daga cikin yaran Lado da aka jikkata an garzaya da shi zuwa babban asibitin Suleja.
KARANTA WANNAN: Ezekwesili: An mayar da rayukan 'yan Nigeria kamar na kiyashi a yau
Wakilin Dailytrust da ya ziyarci inda lamarin ya afku, ya kirga motoci akalla 21 da ke dauke da fastocin Abubakar wadanda 'yan ta'addan suka yi raga raga da su, a wani gidan sayar da man fetur da ke yankin inda suka tsaya don shan mai.
Wani da lamarin ya faru a gabansa, ya ce motocin sun zo ne a jerin gwano daga Sabo Wuse, inda Ado ya ke rike da kujerar shugaban karamar hukumar Tafa. Ya ce akalla motoci 30 ne suka bar gidan man inda suka doshi garin Suleja don yakin zabe, a lokacin ne tawagar dan majalisar wakilan tarayya mai ci a yanzu ta iso wajen.
Kwamandan rundunar 'yan sanda na yankin CSP Iliyasu Kwarbi, ya shaidawa wakilin cewa ba zai iya cewa komai akan lamarin ba har sai ya gana da wadanda lamarin ya shafa.
Babbar Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng