Ana Kukan Kara Kudin Fetur: Gwamnati Ta Sanar da Shirin Kara Haraji a Najeriya

Ana Kukan Kara Kudin Fetur: Gwamnati Ta Sanar da Shirin Kara Haraji a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta ce tana shirin kara kudin haraji na kimar kayayyaki (VAT) daga kashi 7.5 da ake caja yanzu zuwa kashi 10
  • Kwamitin da shugaban kasa ya kafa karkashin Taiwo Oyedele a gyara manufofin kasafi da sake fasalin haraji ne ya bayyana hakan
  • Kwamitin ya ce ya kammala hada daftarin dokar kuma zai gabatar da ita gaban majalisar tarayyar kasar domin amincewarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Taiwo Oyedele, shugaban kwamitin shugaban kasa kan manufofin kasafin kudi da sake fasalin haraji, ya ce kwamitin zai gabatar da wata doka ga majalisar dokoki.

A cewar Taiwo Oyedele, dokar da kwamitin za ta gabatar za ta sa a kara harajin kimar kayayyaki (VAT) daga kashi 7.5 na yanzu zuwa kashi 10.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba Gida Gida ya fusata da aiki, ya kwace kwangilar titi a Kano

Gwamnatin tarayya ta yi magana kan kara kudin VAT
Gwamnatin tarayya za ta gabatar da dokar kara harajin kudin VAT. Hoto: Getty Images, @officialSKSM (X)
Asali: UGC

An yi daftarin sabon harajin VAT

Shugaban kwamitin shugaban kasar ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels a shirinsu na 'Siyasa a yau'.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma ce kwamitin nasa yana kokarin hada haraji da dama a waje daya domin tabbatar da rage harajin a Najeriya.

Taiwo Oyedele ya kara da cewa za a mika dokar harajin da kwamitin ya kammala tsarawa ga majalisar dokokin kasar domin amincewarsu, inji Daily Trust.

Gwamnati za ta kara haraji

Shugaban kwamitin ya ce:

“Muna da manyan matsaloli a batun kudaden harajin da muke samu. Muna da matsaloli a kudaden shigarmu na haraji da wanda ba na haraji ba.
“Lokacin da aka kafa kwamitina, muna da manyan ayyuka guda uku: Na farko mu duba kudaden gudanar da gwamnati, na biyu sauya tsarin kudaden shiga da na uku kadarorin gwamnati.

Kara karanta wannan

"Muna kan aiki," Gwamna ya faɗi matakin da ya ɗauka kan biyan sabon albashin N70,000

"Wannan sabuwar dokar da muke son gabatarwa majalisar dattawa za ta kara kudin haraji daga 7.5% zuwa 10% daga 2025. Ba mu san zuwa yaushe za su amince da dokar ba."

Batun shirin kara kudin harajin dai na zuwa ne a lokacin da aka rahoto cewa kamfanin NNPCL ya kara kudin man fetur daga N555 zuwa N897 a wasu jihohin kasar.

Kano ta tara haraji mafi yawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa jihar Kano ta tara harajin kimar kayayyaki (VAT) wanda ya zarce harajin da jihohin yankin Kudu maso Gabas suka tara gaba daya.

Bayanan da aka samu na VAT daga hukumar tara haraji ta FIRS, sun nuna cewa jihar Kano kadai ta tara N24.4b, fiye da kudaden da jihohi biyar na Kudu maso Gabas suka tara na N20bn.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.