Tsohon Sanatan Arewa da Ake Zargin Ya Yi Lalata da Matar Aure a Bidiyo Ya Magantu

Tsohon Sanatan Arewa da Ake Zargin Ya Yi Lalata da Matar Aure a Bidiyo Ya Magantu

  • Sanata Ishaku Abbo, haifaffen jihar Adamawa ya sake jawo ce-ce-ku-ce a kafofin sada zumunta bayan bullar wani bidiyo a baya-bayan nan
  • A cikin faifan bidiyon an ga wani mutumi da ake zargin Sanata Ishaku Abbo ne yana lalata da wata mata da ake zargin matar aure ce
  • Sai dai tsohon sanatan ya musanta wannan zargi inda ya ce ba shi ne mutumin da ke cikin bidiyon ba tare da yin karin haske a kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Adamawa - Ce-ce-ku-ce ya sake barkewa kan Sanata Ishaku Abbo, haifaffen jihar Adamawa bayan bullar wani bidiyo da ake zargin tsohon sanatan ya na lalata da wata matar aure.

Kara karanta wannan

Rana ta baci: Mai maganin gargajiya ya kashe mutum wajen gwajin maganin bindiga

Idan ba a manta ba, shekaru biyu baya, an zargi Sanata Abbo da cin zarafin wata mata mai shayarwa a wani kantin sayar da kayan jima’i a Abuja.

Sanata Ishaku Abbo ya yi magana kan bidiyon da ke nuna yana lalata da matar aure
Sanata Ishaku Abbo ya nesanta kansa daga bidiyon wani mutumi da ke lalata da matar aure. Hoto: @justeventsonlin
Asali: Facebook

Ana zargin sanata da lalata da matar aure

A cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, an ga wani mutum mai hasken launin fata yana lalata da wata mata da ake zargin Sanata Ishaku ne, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani abin mamaki, an sanya sunan Sanata Abbo a matsayin wanda aka bayyana a cikin faifan bidiyon, zargin da har yanzu ba a tabbatar ba daga wata majiya mai tushe.

Biyo bayan yaduwar bidiyon da kuma yadda ake ta cewa tsohon sanatan ne a ciki, an rahoto cewa Sanata Ishaku ya kira taron manema labarai a kan lamarin.

Sanata ne yake lalata a bidiyo?

Kara karanta wannan

An gano bidiyon Bello Turji yana shan alwashi bayan kwace motocin sulken sojoji

Sanata Ishaku ya musanta cewa shi ne mutumin da ke cikin faifan bidiyon da aka nuna ya na lalata da matar aure 'yar Adamawa kuma mijinta ya na zama a Abuja.

Abbo ya yi kakkausar suka, inda ya ce:

"Ta yaya za ka iya gane mutum ba tare da ganin fuska ko jikinsa ba, sai dai kawai sassan kafafunsa kuma ka zo ka ce Sanata Abbo ne?"

Ishaku Abbo wanda Kotun Daukaka Kara ta kora daga kujerarsa ta sanata ya zargi abokan hamayyarsa na siyasa da daukar nauyin abin da ya kira "salon damfara."

Kotu ta tsige sanatan Adamawa

A wani labarin, mun ruwaito cewa Kotun Daukaka Kara da ke da zama a Abuja, ta rusa nasarar zaben Elisha Ishaku Abbo da aka yi a farkon 2023.

Sanata Ishaku Abbo daga Adamawa ta Arewa ya sha kayi a kotun ne bayan da Amos Yohanna na jam'iyyar PDP ya shigar da kara gaban kotun kan nasarar zabensa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.