Na kama mijina dumu-dumu yana lalata da matar aure - Matar Liman ta sanar da kotu

Na kama mijina dumu-dumu yana lalata da matar aure - Matar Liman ta sanar da kotu

Wata mata, Rebecca Adeniyi, ta sanar da kotun gargajiya da ke zamanta a yankin Igando, jihar Legas, cewa ta kama mijinta turmi da tabarya yana lalata da matar aure.

A cewar Rebecca, mjinta mai suna Yusuf ya gina Masallaci tare da mayar da shi wurin lalata da mata masu aure da marasa aure.

"Na kama shi turmi da tabarya yana lalata da daya daga cikin matan auren da ke zuwa Masallacinsa. Na rike matar, na yaga mata tufafi.

"Na so na kwarmata maganar kowa ya sani, amma sai ya fara rokona a kan na rufa wa matar asiri don kada mijinta ya sake ta.

"Jama'a sun kaurace wa Masallacin saboda halayen mijina na banza, amma yanzu kuma ni yake zargi da korar mabiyansa.

"Tun bayan lokacin da na kama shi ya sauya min, ya daina bani kulawa, ya daina bani kudin abinci," a cewar Rebecca, uwar 'ya'ya hudu.

Na kama mijina dumu-dumu yana lalata da matar aure - Matar Liman ta sanar da kotu

Na kama mijina dumu-dumu yana lalata da matar aure - Matar Liman ta sanar da kotu
Source: UGC

Malamin addinin, mai shekaru 47 a duniya, ya amsa laifin cewa yana lalata da matan aure da ke zuwa Masallacinsa, sai dai, ya dora laifin yin hakan a kan sharrin shaidan.

"Na roki mata ta a kan ta yafe min, na daukar mata alkawarin cewa ba zan kara ba, amma duk da haka sai da ta tona min asiri," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Na ji dadin dakatar da Oshiomhole - Mataimakin shugaban APC na kasa yankin arewa

Liman Yusuf ya zargi matar tasa da yin lalata da mijin matar da ta kama shi yana lalata da ita a cikin Masallacinsa.

"Yanzu haka matata tana zaune ne da mijin matar da ta kama mu tare," a cewar Liman Yusuf.

Yusuf ya roki kotun a kan kar ta raba auren da ke tsakaninsa da matarsa, kamar yadda ta nema.

Bayan kammala sauraron kowanne bangare, shugaban kotun, Mista Adeniyi Koledoye, ya tsayar da ranar 20 ga wata domin yanke hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel