Awanni bayan Harin 'Yan Boko Haram, Sojoji Sun Dura Garin da Aka Kashe Mutane 87
- Rahotanni sun bayyana cewa sojojin Najeriya sun kwashe gawarwakin mutanen 37 daga cikin 87 da ake zargin mayakan Boko Haram sun kashe
- Mataimakin gwamnan Yobe, Idi Barde Gubana zai jagoranci jami’an gwamnati domin halartar jana’izar mutanen 37 a fadar Sarkin Babbangida
- Tun da fari an ruwaito cewa 'yan ta'addan Boko Haram sun kashe gomman mutane a harin da suka kai Mafa da ke yankin Arewa ta gabas
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Yobe - An kwashe gawarwakin mutanen 37 da mayakan Boko Haram suka kashe daga garin Mafa da ke karamar hukumar Tamuwa a jihar Yobe.
Majiyoyi sun bayyana cewa an kai gawarwakin mutanen da aka kashe zuwa babban asibitin Babbangida kafin a yi jana’izarsu da karfe 10 na safe.
Majiyoyi daga al’ummar yankin sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa 'yan ta'addan Boko Haram sun kashe akalla mutane 87.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun kwaso gawarwaki a Yobe
Mataimakin gwamnan Yobe, Idi Barde Gubana zai jagoranci jami’an gwamnati domin halartar jana’izar a fadar Sarkin Babbangida, hedikwatar karamar hukumar Tarmuwa.
Wata majiya ta bayyana cewa:
“Mun samu tabbacin cewa sun kashe akalla mutane 87. Ba za mu iya nuna muku gawarwakin wadanda aka kashe ba saboda wasu sun mutu a daji, har sojoji sun kasa gano su."
Hare-haren mayakan Boko Haram
Majiyar ta ci gaba da cewa:
“Ya zuwa yanzu gawarwaki 37 suna babban asibitin Babbangida bayan da sojoji suka kwashe su daga cikin garin da abin ya faru, sannan kuma za a birne gawarwakin da suka rube a wurin.”
A watan da ya gabata, mutane biyu aka kashe tare da daidaita iyalai 475 a wani hari da mayakan Boko Haram suka kai wanda ya shafi mutum 2,390 a gundumar Mafa.
Boko Haram ta kai hari Yobe
Tun da fari, Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa 'yan ta'addan Boko Haram sun kashe gomman mutane a harin da suka kai Mafa da ke jihar Yobe.
An ce ‘yan ta’addan na Boko Haram sun kashe mutanen kauyen da dama, musamman manoma, tare da kona gidaje da shaguna a garin da ke karamar hukumar Tamuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng