Bayan garkuwa da mutane 35, yan Boko Haram sun kai hari Mafa
Wasu da ake zargin yan Boko Haram ne sun kai hari ranar Asabar kauyen Ajiri dake kramar hukumar Mafa, jihar Borno inda suka hallaka rayuka da dukiyoyin jama'a.
Vanguard ta ruwaito majiya da cewa yan ta'addan sun kai harin ne da yammacin Asabar.
Wannan na faruwa ne jim kadan bayan yan ta'addan sun kai hari hanyar Maiduguri zuwa Damaturu inda suka hallaka akalla mutum 5.
Kauyen Ajiri na da nisan kilomita 50 da Maiduguri, a karamar hukumar Mafa, garin gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum.
An dade babu jama'a a garin kafin gwamnan jihar ya gina gidaje 500 kuma ya bukaci yan sansanin gudun hijra su koma gida a tsakiyar shekaran nan.
KU KARANTA: Matasan Kataf sun yi martani, sun halaka mace 1 da yara 6 a Kaduna
KU KARANTA: Masari karya yake, ba damu aka tattauna da yan bindigan da suka saci daliban Kankara ba: Miyetti Allah
Kun ji cewa akalla matafiya 35 ne yan ta’addan Boko Haram suka yi garkuwa da su a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.
Majiyoyin soji wadanda sun bayyana cewa yan ta’addan sun far ma ayarin matafiyan a kusa da Garin Kuturu da ke Jakana da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Juma’a.
An tattaro cewa yan ta'addan wadanda suka kasance cikin kayan sojoji, sun sanya shinge a babbar titin da motocin Hilux guda biyar kafin suka tafi da fasinjojin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng