Sojoji Sun Cafke Masu Kai Wa ‘Yan Ta'adda Miyagun kwayoyi a Arewa Maso Gabas
- Rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa (MNJTF) ta yi nasarar cafke mutane biyu da ake zargi da kai wa 'yan ta'adda miyagun kwayoyi
- Rundunar ta bayyana cewa an kama mutanen a hanyar Kekeno zuwa Cross Kauwa a jihar Borno kuma a kwato kwayoyi da tabar wiwi
- Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, kakakin rundunar MNJTF ya kara da cewa sojojin sun ceto wasu mata uku da jaririn a yayin atisayen
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Rundunar sojojin hadin gwiwa ta MNJTF ta ce ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da kai wa mayakan Boko Haram da ISWAAP miyagun kwayoyi a yankin tafkin Chadi.
An kuma yi zargin cewa wadanda aka kaman suna safarar kakin jami'an tsaro da wasu kayayyaki ga 'yan ta'addan.
An cafke aminan 'yan Boko Haram
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, kakakin rundunar MNJTF ya fitar ranar Alhamis a Maiduguri, a cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce dakarun rundunar sun kama daya daga cikin wadanda ake zargin a kan hanyar Kekeno zuwa Cross Kauwa a jihar Borno.
Laftanar Kanal Olaniyi ya kara da cewa dakarun sun kwato kwato kayayyakin maye masu yawa da kuma kunshin tabar wiwi 198.
Borno: An ceto mata da jariri
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kakakin rundunar ya ce sojojin sun kuma ceto mata uku da jariri daya, wadanda ake zargin 'yan uwa ne ga 'yan ta'addar.
A cewarsa, matan sun yi ikirarin cewa sun tsero ne daga mabuyar ‘yan ta’addan a kudancin tsibirin Tafkin Chadi a karamar hukumar Marte a jihar Borno.
“A halin yanzu ana duba lafiyar matan da jaririn tare da kuma tattara bayanansu."
- A cewar Laftanar Kanal Olaniyi.
An kama makusantan 'yan ta'adda
A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar sojojin hadin gwiwa ta MNJTF ta ce dakarunta sun kama iyalai da masu taimakawa mayakan Boko Haram.
Rundunar ta ce an kama aklla mutane 900 da ke da alaka da 'yan ta'addan yayin da dakarunta ke ci gaba da karya lagon 'yan Boko Haram da ISWAP a yakin Tafkin Chadi.
Asali: Legit.ng