Babu Sunan Kano, Kaduna a Jerin Jihohin Najeriya 8 Mafi Tsafta a Shekarar 2024
- A yayin da watan Agustan 2024 ke shirin karewa, kungiyar nazarin fasaha ta kasa ta fitar da jerin jahohi mafi tsafta a Najeriya
- Rahoton NTSG ya nuna cewa jihohi takwas ne mafi tsafta a kasar nan, bayan da suka tabbatar da muhallansu sun samu kulawa
- Jihohin da suka samu shiga wannan jerin sun kara fito da ma'anar karin maganar Bahaushe da ke cewa 'kwalliya ta biya kudin sabulu'
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kungiyar nazarin fasaha ta kasa (NTSG) ta fitar da jerin jahohi takwas mafi tsafta a kasar nan a shekarar 2024.
Jihohin da suka samu shiga wannan jerin sun ba da fifiko ga tsafta kuma sun kara fito da ma'anar karin maganar nan na cewa 'kwalliya ta biya kudin sabulu.'
Rahoton Tribune ya nuna cewa jihohin sun aiki tukuru wajen tabbatar da cewa muhallansu sun samu kulawar da ake bukata domin hana yaduwar cututtuka da gurbatar iska.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duba jerin jihohin Najeriya mafi tsafta a 2024 kamar yadda rahoton kungiyar NTSG ya nuna.
Jihohi 8 mafi tsafta a Najeriya
1. Jihar Akwa Ibom
Jam’iyyar PDP mai mulki ta kashe makudan kudade a wajen samar da kayayyakin tsaftar muhalli domin ci gaba da kula da tsaftar jihar.
Jihar mai arzikin man fetur a yankin Kudu maso Kudu na da tsare-tsare na magance gurbatar muhalli tare da shirya wayar da kan jama’a a kan muhimmancin tsaftar muhalli.
2. Jihar Ebonyi
Jihar Ebonyi da ke a Kudu maso Gabas ta dukufa wajen ganin an zubar da shara a inda ya kamata, tare da kawo tsare-tsaren tsaftar muhalli a jihar.
Jihar wadda ke karkashin jagorancin gwamnan jam’iyyar APC ta yi gine ginen zamani domin dorewar tsaftar muhalli da kuma gujewa illar gurbatar muhalli.
3. Jihar Cross River
Abin da ke zuwa a zuciyar mutane yayin ambaton sunan Calabar, babban birnin jihar Cross River shi ne 'birni mafi tsafta da kyawun muhalli'.
Cross River, jiha ce da ke a Kudu maso Kudu wacce a ko da yaushe ke jaddada muhimmancin samar da yanayi da muhalli mai kyau.
Gwamnatin jihar ta kuma kaddamar da ayyuka daban-daban na inganta dashen itatuwa domin magance zaizayar kasa da samar da iska mai kyau ga jama'a.
Sauran jihohi mafi tsafta a Najeriya
4. Jihar Enugu
5. Jihar Delta
6. Jihar Edo
7. Jihar Filato sai
8. Birnin tarayya Abuja
A cikin wannan jerin sunayen, ba a ga sunan jihar Kano, kuma babu sunan jiha ko daya daga Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.
Jihohi mafi tsadar abinci
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar NBS ta bayyana cewa jihar Kogi ce a kan gaba a jihohin Najeriya mafi tsadar kayan abinci a Mayun 2024.
Bayanin na kunshe ne a cikin rahoton NBS na hauhawar farashin kayayyaki wanda ya nuna cewa kayan abinci sun yi tsada a Mayun zuwa 40.66%.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng