Anyi yar kure: duba jihohin da suka fi kazanta da tsafta a Najeriya gaba daya

Anyi yar kure: duba jihohin da suka fi kazanta da tsafta a Najeriya gaba daya

Jihohin Kogi, Osun, Nasarawa, Zamfara da Kebbi ne kan gaba a jerin jihohin Najeriya da suka kazantar gari, datti da abin kyama, yayin Da jihohin Akwa Ibom, Cross River, Abuja, Rivers da Niger suka ciru tuta a tsakanin jihohin Najeriya a maganan tsaftar gari.

Jaridar The Sun ta ruwaito wata kungiya mai zaman kanta, Clean Up Nigeria, CUN ce ta bayyana haka a cikin wata rahoto da ta fitar bayan dogon bincike da tattara bayanai da tayi tun daga watan Oktobar 2017 zuwa Oktoban 2018.

KU KARANTA: Kowa ya debo da zafi: Wani Uba ya yi ma mutumin da yayi ma diyarsa fyade dandaka

Anyi yar kure: duba jihohin da suka fi kazanta da tsafta a Najeriya gaba daya
Kazanta
Asali: UGC

Majiyar Legit.com ta ruwaito CUN ta rarraba maki ga jihohin Najeriya duba da iya tsaftar dake akwai a kowacce jaha, jihohin Kogi da Osun na da maki 11 cikin dari, Nassarawa 12.2, Zamfara 14.2 sai kuma jahar Kebbi dake da maki 14.2.

A hannu guda kuma, jahar Akwa Ibom ce ta ciri tuta a wajen tsaftar gari a Najeriya gaba daya, inda ta kasance jaha daya tilo dake da maki 78, mabi mata, jahar Cross Rivers 64, sai Abuja da maki 58, Rivers ce ta hudu da da maki 37, jahar Neja ta biyar mai maki 35.2.

Rahoton ya bayyana cewa kungiyar ta zagaye duk jihohin Najeriya talatin da shida da babban birnin tarayya Abuja, tare da kwararrun masana ilimin muhalli, wanda sune suka raba maki ga jihohin duba da yanayin tsaftar.

Shugaban CUN, Ene Baba Owoh ya bayyana cewa suna lura da tsaftar jihohi a duk wata uku uku, sa’annan suna amfani da ma’aunai guda biyar wajen sa ido. “Ya kamata gwamnatin tarayya, jihohi, kananan hukumomi da jama’a su kaddamar da halin ko ta kwana wajen kawar da illar datti da kazanta a Najeriya.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel