Lafiya jari: Shin kana fama da cutar Olsa? Ka gwada sinadarin 'yayan kankana

Lafiya jari: Shin kana fama da cutar Olsa? Ka gwada sinadarin 'yayan kankana

- Bincike da dama sun gudana kan amfani da 'yayan itatuwa, musamman ma kankana, wajen rage kamuwa da cutar nauyin jiki, ciwon sukari, da ciwon zuciya ko yankewar jiki

- Sai dai, masana kimiyya sun tabbatar da amfanin kankana wajen magance cutar Olsa, wacce kowa ya fi sani da cutar 'yunwa'

- Ko da aka gwada 'yayan kankana da maganin 'Renitidine,' ya nuna amfanin 'yayan kankana da ma'auni 4000mg/kg, da cewa za a iya amfani da 'yayan kankana wajen magance cutar olsa

Kankana, na daya daga cikin 'yayan itatuwan da suka yi suna a wannan duniya tamu. A yayin da muke jin dadi tare da shaukin shan wannan dan icce, mukan rika mantuwa muna tuya babu albasa, ma'ana, mukan riga shan kankanar ba tare da cin 'yayan da ke a cikinta ba, ba tare da munsan dumbin magungunan da ke tattare da 'yayan ba.

Bincike da dama sun gudana kan amfani da 'yayan itatuwa, musamman ma kankana, wajen rage barazanar kamuwa da cutar nauyin jiki da dai sauran cututtuka da suka hada da ciwon sukari, da ciwon zuciya ko yankewar jiki.

Sai dai, masana kimiyya sun tabbatar da amfanin kankana wajen magance cutar Olsa, wacce kowa ya fi sani da cutar 'yunwa'. Sun yi amfani da 'yayan da ke jikin kankanar, inda suka gudanar da bincike mai zurfi akai, ta hanyar gwaji a dakin sarrafa magunguna da gano cututtuka dama hanyoyin magance su, inda suka fara yin gwajin akan beraye.

KARANTA WANNAN: Antoni Janar: Dalilinmu na rabawa talakawa $322.5m da Abacha ya boye tun a zamaninsa

Lafiya jari: Shin kana fama da cutar Olsa? Ka gwada sinadarin 'yayan kankana
Lafiya jari: Shin kana fama da cutar Olsa? Ka gwada sinadarin 'yayan kankana
Asali: UGC

Berayen da aka yiwa gwajin da sinadaren 'yayan kankana, sun nuna samun waraka daga cutar Olsa, rage sinadrin 'gastric acid' da kuma nesanta daga kamuwa daga cutar ta Olsa.

Ko da aka gwada 'yayan kankana da 'Renitidine,' maganin da ya shahara wajen magance cutar olsa, hakan ya nuna girman amfanin 'yayan kankana da ma'auni 4000mg/kg, wanda ke nuni da cewa za a iya amfani da 'yayan kankana wajen magance cutar olsa.

Babban amfani 'yayan kankanar, ba zai wuce yadda ba sa dauke da wata illa ba, sabanin mafi yawancin magunguna da ake hadawa a 'Labs', da ke iya haifar da wata matsalar ta daban, kama daga ciwon kai, amai da gudawa, ciwon jiki da ciwon kashi.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Kungiyar kwadago ta janye shiga yajin aiki, gwamnati za ta biya N30,000

Daga cikin amfanin 'yayan kankana da ita kanta kankanar, akwai rage karfin cutar ciwon sukari, yaki da kwayoyin cutuka da ka iya kawo farmaki nan take, karfafawa zuciya wajen gudanar da ayyukanta, hanyar karuwar karfi da ruwa a jiki wanda ke rage kamuwa da cutar asma, haka zalika kankana na taimakawa wajen rage kibar jiki.

Ana amfani da man 'yayan kankana wajen girka abinci da kuma hada kayan kwalliya da gyaran jiki. Sinadarin man na kashe tsutsar ciki da ta hanji. Kamar dai yadda binciken masana kimiyya ya nuna, sinadarin da ke dauke a 'yayan kankana, na iya zama madadin maganin cutar, 'Ranitidine,' da aka saba amfani da shi.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel