"Mu na Azumi don Rage Ci," Mazauna Kaduna Sun Koka kan Hauhawar Farashi

"Mu na Azumi don Rage Ci," Mazauna Kaduna Sun Koka kan Hauhawar Farashi

  • Mazauna jihar Kaduna sun koka kan yadda ake samun tashin farashin kayan abinci a kasuwannin jihar
  • Wasu daga cikin mazauna jihar sun ce ba su iya cin abinci sau uku a rana saboda tsadar kayan abinci a kasuwa
  • A zantawarsu da manema labarai, wasu daga cikin mutanen jihar sun ce albashin N100,000 ba ya isar su a wata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Wasu daga cikin mazauna jihar Kaduna sun koka kan yadda ba sa iya cin abinci su koshi a gidajensu.

Mazauna jihar sun ce yanzu ba sa iya cin abinci sau uku a rana, wannan ya biyo bayan hauhawar farashin kayan abinci da ake samu.

Kara karanta wannan

Yayin da ambaliya ke rusa gidajen Kaduna, gwamnatin Uba Sani za ta gina sabon birni

Kaduna
Mazauna Kaduna sun koma kan tsadar abinci Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa Fatima Idris, wata matar aure a jihar ta ce mai gidanta ta umarce ta da girki sau biyu a rana - karin kumallo da abincin dare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce dole ta sa su rage cin abinci da sauran dawainiyar saboda matsalar tattalin arziki da ake fama da shi a kasar nan.

Mazauna Kaduna na azumi domin rashin abinci

Wasu daga cikin mazauna jihar Kaduna sun ce su kan yi azumin nafila na kwana biyu domin samun lada da kuma rage cin abinci saboda tsadarsa

Muhammad Bello ya ce ya kan yi sahur da ruwa da dabino, amma ya kan ci abinci mai kyau da bude baki domin inganta lafiyar jikinsa, Jaridar Vanguard ta wallafa labarin.

An daina yi wa baki tayin abinci

Wasu daga cikin mazauna jihar Kaduna sun rage yi wa baki tayin abinci saboda tsadarsa, kuma ba kullum ake dafawa ba.

Kara karanta wannan

Magani na gagarar talaka: Masu ciwon sukari sun nemi alfarma wajen Shugaba Tinubu

Wata mazauniyar jihar ta bayyana cewa yanzu sau biyu kawai su ke cin abinci domin tattala N100,000 da mai gidanta ke samu a matsayin albashi.

Farashin gas ya hau a Kaduna

A baya kun ji cewa farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabo a jihar Kaduna inda ake sayar da kowace lita a kan N1,000 a wajen wasu yan bunburutu a jihar.

Wannan ya biyo bayan karancin fetur din yayin da ake samun dogayen gidajen mai a gidajen mai da ke jihar Kaduna, lamarin ya jefa jama'a cikin mugun hali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.