NiMET: Jerin Jihohin Arewa 6 da Za a Tafka Ruwa da Iska Mai Karfi, an Gargadi Mutane

NiMET: Jerin Jihohin Arewa 6 da Za a Tafka Ruwa da Iska Mai Karfi, an Gargadi Mutane

  • An gargadi mazauna jihohin Kano, Katsina, Sokoto, Kebbi, Kaduna da Zamfara da su guji yankunan da suka saba ganin ambaliyar ruwa
  • Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta fitar da sanarwar gargadin ne a ranar Litinin, inda ta ce jihohin za su fuskanci ruwa mai karfi
  • Hukumar NiMET ta yi hasashen cewa tsawa da iska mai karfi tare da ruwan sama kamar da bakin kwarya zai zuba a kwanaki masu zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ta fitar da sanarwar gargadi ga wasu jihohin Arewacin kasar guda shida.

NiMET ta gargadi jihohin da su shirya ganin tsawa da iska mai karfi yayin da ruwan sama kamar da bakin kwarya zai zuba a kwanaki masu zuwa.

Kara karanta wannan

Sunayen gwamnonin Arewa da ake zargin sun kitsa zanga zangar adawa da Tinubu, Rahoto

Hukumar NiMET ta gargadi wasu jihohin Arewa 6 kan ruwa kamar da bakin kwarya
NiMET: Ana hasashen ruwa kamar da bakin kwarya zai jawo ambaliya a wasu jihohin Arewa 6. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Tsawa da ruwa a jihohi 6

Gargadin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar gwamnatin ta fitar ranar Litinin, 26 ga Agusta a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar hukumar da ke da alhakin hasashen yanayi, ta ce jihohin arewa abin ya shafa su ne:

  1. Kano
  2. Katsina
  3. Sokoto
  4. Kebbi
  5. Kaduna
  6. Zamfara

NiMET ya ta yi hasashen cewa ruwan saman da za a tafka kamar da bakin kwarya zai iya haifar da ambaliya.

An shawarci mazauna wadannan yankuna da su yi taka tsantsan da kuma shirya kansu domin fuskantar yanayin mai cike da kalubale.

NiMET ta ba da matakan kariya

1. Ruwan sama mai yawa na iya haifar da ambaliya; an shawarci mazauna jihohin da su guji wuraren da suka saba ganin ambaliyar ruwa.

2. A bi ƙa'idodin kare kai da hukumomin da abin ya shafa suka bayar.

Kara karanta wannan

Rahoton UNICEF: Gwamna a Arewa zai binciki badakalar sayar da abincin jarirai

3. An shawarci jama'a da ma'aikatan jirgin sama da su sami sababbin rahotanni na hasashen yanayi daga NiMet domin tsara ayyukansu yadda ya kamata.

4. Ci gaba da samun bayanai game da sauyin yanayi daga NiMet ta ziyartar shafinta na yanar gizo a http://nimet.gov.ng

Za a sheka ruwa a jihohi 26

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ta yi hasashen cewa za a zabga ruwan sama a wasu jihohi 26 na Najeriya.

Awanni 24 ake tunanin za a dauka ana tsula ruwan sama a jihohin Kudu da Arewa, wanda har ake hasashen ruwan na iya jawo ambaliya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.