Sanusi II, Obasanjo, Gowon da Wasu Shugabanni da Suka Koma Aji Neman PhD
Ba sabon abu ba ne a ji manyan mutane sun koma makaranta domin yin digirin farko, na biyu ko kuwa na uku watau PhD.
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Ganin Muhammadu Sanusi II ya zama dakta, Legit Hausa ta waiwayi baya, ta duba sauran manyan da ya bi irin sahun nasu.
Shugabannin da suka koma neman PhD
1. Yakubu Gowon yana da PhD
Janar Yakubu Gowon ya tare a Ingila bayan juyin mulkin da aka yi masa, hakan ta sa ya samu damar komawa kara ilmi a jami’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon shugaban kasar ya samu digirin PhD a jami’ar Warwick a lokacin da sojojin da suka hambarar da shi su ke mulkin Najeriya.
Samun wannan digiri ya taimakwa Yakubu Gowon ya zama babban malami a jami’ar Jos, ya rika koyar da ilmin siyasa a 1980s.
2. Olusegun Obasanjo ya yi PhD
Shekaru bayan ya bar mulki, Premium Times ta rahoto cewa Olusegun Obasanjo ya samu shaidar digirin PhD a jami’ar NOUN.
A lokacin yana shugaban Najeriya ne Cif Obasanjo ya kafa jami’ar tafi-da-gidanka, ya yi digirin nasa ne a ilmin addinin kiristanci.
Deji Ayegboyin, Mustapha Adejoro, Nebath Tanglang, Samaila Mande, Godwin Akper da Cletus Gotan suka duba aikinsa a jami'ar.
3. Nasir El-Rufai ya fara PhD
A 2017 Punch ta rahoto Nasir El-Rufai yana digirinsa na PhD a wata jami’ar kasar Nederlands a kan ilmin mulki da tsare-tsare.
Babu labarin ko ya kammala karatun, amma kafin ya bar mulkin Kaduna an ji yana cewa yana fatan karasa karatun ko ya tare a Maastricht.
4. Rabiu Kwankwaso ya samu PhD a Indiya
Rabiu Musa Kwankwaso yana shekaru fiye da 60 aka ji ya kammala digirinsa na PhD a ilmin ruwa a jami’ar Shardah da ke kasar Indiya.
Binciken The Cable ya nuna Kwankwaso ya fara karatun ne a 2018 ya gama a 2022, ya yi bincikensa a kan noman rani a Arewacin Najeriya.
Sanusi II ya yi PhD babu gyara
Ana da labarin cewa jami'ar SOAS da ke kasar Ingila ta yi wa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II albishiri kammala digirin PhD.
Abin sha'awar shi ne Sarki Kano ya gabatar da bincikensa a kan ilmin shari'a ba tare da an samu wani kuskure a cikin kundinsa nasa ba.
Asali: Legit.ng