Ba a Gama da Kwangilar Magani ba, Gwamnatin Kano Ta Bankado Badakalar N660m

Ba a Gama da Kwangilar Magani ba, Gwamnatin Kano Ta Bankado Badakalar N660m

  • Gwamnatin Kano ta sake bankado wata sabuwar badakalar N660m da ta shafi samar da ruwan sha a kananan hukumomi 44 na jihar
  • An ruwaito cewa N660m din na daga cikin N1.1bn da Gwamna Abba Yusuf ya ware domin samar da ruwa da magunguna a jihar
  • Sai dai wani bincike da hukumar yaki da rasha ta jihar ke gudanarwa ya nuna cewa babu alamar an yi aikin da aka warewa kudin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Bincike kan badakalar kwangilar magunguna na kananan hukumomin jihar Kano ya sake daukar sabon salo bayan gwamnatin jihar ta gano wata sabuwar badakala.

An ce masu bincike kan yaki da rashawa sun fara bin diddigin wata N660m da ake zargin an karkatar da ita a kwangilar samar da ruwan sha a Kano.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta fadi abin da zai faru kan zargin badakalar kwangilar magani

Gwamnatin Kano ta fara bincike kan zargin karkatar da kudin samar da ruwan sha
Gwamnatin Kano ta fara bin diddigin N660m na kwangilar samar da ruwan sha. Hoto: Muhuyi Magaji Rimingado/Facebook, Claudiad/Getty Images
Asali: UGC

An rabawa kananan hukumomin Kano N1.1bn

Jaridar Daily Trust da ta fitar da rahoton ta ce N660m din na daga cikin N1.1bn da gwamnatin Abba Yusuf ta amince a kashewa kananan hukumomi 44 na jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce Gwamna Yusuf ya fitar da kudin ne da nufin magance matsalar ruwan sha da karancin magunguna da ake fuskanta a kananan hukumomin.

Kowace karamar hukuma za ta samu N25m daga cikin N1.1bn da aka ware, kuma za a gudanar da aikin ne a watan Agusta, Satumba da Oktoba.

Kano: Badakalar kwangilar magunguna

Daga cikin N25m da aka ba kowace karamar hukuma a watan Agusta, an gano cewa an umarci kowanne ciyaman ya tura N10m ga kamfanin Novomed.

An ruwaito cewa kananan hukumomin za su turawa kamfanin kudin ne da cewar zai samar masu da magunguna, lamarin da aka gano an karya dokar ba da kwangila.

Kara karanta wannan

Badakalar kwangila: An cafke 'Dan uwan Kwankwaso, Hadimin Abba da wasu mutum 4

Hukumar yaki da rashawa ta Kano (PCACC) ta cafke wasu da ake zargin suna da hannu a kwangilar magungunan, ciki har da dan uwan Rabiu Musa Kwankwanso.

An bankado badakalar ruwan shan N660m

To sai dai kuma, jaridar ta ruwaito cewa binciken hukumar ya dauki sabon salo a ranar Talata, inda ta gano akwai kimanin N660m da ake zargin an karkatar na samar da ruwa.

An ce ana zargin an yi sama da fadi da N660m da aka ware domin gyara famfunan tuka tuka a kananan hukumomi 44 na jihar.

Wani daga cikin masu binciken da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

"Shugaban kungiyar kananan hukumomin jihar ya yi ikirarin cewa an kashe kudin wajen gyara famfunan tuka tuka, amma babu wata alama ta cewa an kashe N660m a gyara ruwan."

Gwamnati ta cafke dan uwan Kwankwaso

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano ta cafke Musa Garba, wani dan uwan Sanata Rabiu Kwankwaso bisa zarginsa da hannu a badakalar kwangilar magani.

Kara karanta wannan

Airbus A330: Abin da ya kamata ku sani game da sabon jirgin shugaban kasar Najeriya

Hukumar yaki da rashawa ta Kano, PCACC ta cafke wani shugaban karamar hukuma da mutane uku bisa zargin sun karya dokar bayar da kwangila.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.