Yadda Zanga Zanga Ta Hana Gwamnati Kara Kudin Wuta, Ministan Tinubu Ya Magantu
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ana kashe Naira 120 domin samar da kilowatt 1 na wutar lantarki a kowacce awa
- Ministan wutar lantarki, Cif Adebayo Adelabu wanda ya bayyana hakan ya ce kudin da 'yan Najeriya ke biya na wuta ya kasa
- A cewar ministan, ma'aikatar wuta ta yi niyyar gabatar da sabon karin kudin wutar amma zanga-zangar da aka yi ta kawo cikas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ministan wutar lantarki, Cif Adebayo Adelabu, ya ce ana kashe N120 domin samar da kilowatt 1 na wutar lantarki a kowacce awa.
Cif Adebayo ya yi nuni da cewa wannan dalilin ne ya sa gwamnatin tarayya ke kashe kudade masu yawa wajen biyan tallafin wutar.
Ya yi wannan jawabi ne a wata ziyarar sa-ido da ‘yan majalisar wakilai kan harkokin wutar lantarki suka kai ofishinsa da ke Abuja, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati ta magantu kan samar da wuta
Ministan ya ce kudin bai hada da sauran kudaden da kamfanonin rarraba wutar lantarki ke biya ba a masana’antar samar da wuta ta Najeriya (NESI).
“Wadanda ke a 'Band A' suna biyan N209 yayin da 'Band B' ke biyan N65. Amma kudin da ake samar da kilowat 1 kowacce awa ba ya gaza N120.
"Don haka duk wanda ke biyan N65 ko N58 yana biyan kasa da kudin da gwamnatin tarayya ke bayarwa na tallafin kudin wutar."
- A cewar Cif Adebayo.
Zanga-zanga ta hana kara kudin wuta
Jaridar Daily Trust ta ruwaito ministan ya kara da cewa idan ba domin zanga-zangar da aka yi a baya-bayan nan ba, da ma’aikatar ta kara kudin wuta ga 'yan kasar.
“Watakila nan da watanni 6 masu zuwa, za mu iya zuwa wurin shugaban kasa mu gabatar da sabon tsari na kayyade kudin wutar, amma dai ba mu tsayar da lokaci ba.
“Ba a jima da gama zanga-zangar yunwa a fadin kasar ba, kuma ba ma son wani abu da zai jawo wata zanga-zangar don haka za mu jinkirta."
- A cewar ministan.
Gwamnati ta magantu kan rage kudin wuta
A wani labarin, mun ruwaito cewa ministan wutar lantarki, Cif Adebayo Adelabu ya ba da sharadi na janye karin kudin wutar lantarki da aka yi.
Ya bayyana cewa N225 a kowanne kilowat da masu amfani da lantarki ke biya a rukunin Band A zai ragu idan farashin dala ya dawo kasa da N1,000.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng