Magidanta Sun Fara Samun Saukin Girki, Farashin Gas Ya Rikito Kasa da 14.23% a Najeriya
- Hukumar kididdiga ta Najeriya (NBS) ta fitar da rahoton farashin gas din girki da aka fi sani da LPG na watan Yulin 2024
- Rahoton hukumar ya nuna an samu karyewar farashin gas din a watan Yuli da 14.23% idan aka kwatanta shi da na Yuni
- A zantawarmu da wata Amina Lawal daga Kaduna, ta ce ta sayi kilo 10 na gas din girki a kan N11,886.5, buhun gawayi ya kai N4,500
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Magidanta sun fara samun sauki yayin da farashin cika ma'ajiyar gas din girki mai nauyin 5kg ya ragu da kaso 14.23 a Yuli.
Rahoton hukumar NBS na kan farashin gas din girki da aka fi sani da LPG ya nuna cewa an sayar da 5kg na gas din kan N5,974.54 a Yuli maimakon N6,966.03 a Yuni.
Sai dai jaridar The Guardian ta ruwaito cewa wannan ragin da aka samu bai yi tasiri kan farashin gas din na shekara-shekara ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar rahoton, an sayar da gas din LPG kan N4,072.87 a watan Yulin 2023, wanda ke nufin cewa farashin na wannan shekarar ya karu da kashi 46.69.
Farashin gas din girki a wasu jihohi
Jaridar Leadership ta rahoto cewa jihar Borno ce ta fi ko ina tsadar iskar gas din girki a watan Yuli kamar yadda NBS ta nuna.
An ce ana cika ma'ajiyar gas din mai nauyin 5kg a kan N7,088.59 a jihar Borno, sai kuma Yobe da ke binta a baya, inda ake sayar da shi kan N6,935.50.
A jihar Sokoto kuwa, farashin gas din ya kai N6,750 a watan Yuli. Amma NBS ta ce Delta, Zamfara da Kogi ne aka fi samun arhar gas din.
A Delta, NBS ta ce ana sayar da gas din a kan N5,392.86, sai kuma N5,431.25 a Zamfara da kuma N5,560.63 a Kogi.
Farashin gas a Kaduna da ra'ayin jama'a
A jihar Kaduna, Amina Lawal ta shaidawa Legit Hausa cewa ta sayi kowanne kilo na gas din girki a kan N1,186.65 a ranar Litinin, 19 ga Agusta.
Amina Lawal ta ce sai da ta biya N11,886.5 ta sayi 10kg na gas din, sabanin 12kg da ta saba saye saboda tsadar da ya yi.
A cewarta, gas din a yanzu ya fi gawayi amfani saboda lokacin damina da ake ciki, yayin da ta ce shi kan shi buhun gawayin ya kai N4,500 a unguwar da ta ke zama a Kaduna.
Gwamnati ta dakatar da fitar da LPG
A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnarin tarayya ta sanar da dakatar da fitar da gas din kirgi zuwa kasashen waje da nufin wadatar da 'yan kasuwar gas din na cikin gida.
A cewar gwamnatin tarayyar, dakatar da fitar da gas din zai taimaka wajen gas din ya wadata wanda hakan zai sa farashinsa ya karye yayin da 'yan kasar ke kukan tsadarsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng