Bikin Isese: Gwamnonin Najeriya 4 Sun Ayyana Talata Matsayin Ranar Hutu a Jihohinsu

Bikin Isese: Gwamnonin Najeriya 4 Sun Ayyana Talata Matsayin Ranar Hutu a Jihohinsu

  • Gwamnoni hudu na wasu jihohin Kudu maso Yamma sun ayyana ranakun hutu domin murnar ranar Isese a ranar 20 ga Agustan nan
  • Gwamnatocin Legas, Osun, Oyo da Ogun sun ayyana Talata 20 ga watamatsayin ranar hutun yayin da suke nuna muhimmancin ranar
  • Ranar Isese tana dauke da nau'ikan bukukuwan al'adun da Yarabawa ke gudanarwa har a Cuba, Brazil, Amurka, Benin da sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gwamnatocin Legas, Osun, Oyo da Ogun sun ayyana Talata 20 ga watan Agusta a matsayin ranar hutu domin tunawa da Ranar Isese.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wasu sanarwa daban-daban da kwamishinonin yada labarai na kowace jiha suka fitar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Ana cikin tashin hankali a Sokoto, wa'adin karbo Sarkin Gobir ya kare

Gwamnatocin jihohin Kudu maso Yamma sun ba da hutun ranar Isese
Bikin Isese: Gwamnonin jihohi 4 na Kudu maso Yamma sun ba da hutun kwana 1. Hoto: @gboyegaakosile
Asali: Twitter

Muhimman abubuwa game da Ranar Isese

Ranar Isese tana nufin nau'ikan bukukuwan al'adun da Yarabawa ke gudanarwa a Najeriya da Cuba, Brazil, Amurka, Benin, da sauran kasashe, inji rahoton The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kabilar Yarabawa ita ce kusan kashi 35 mutanen Najeriya kuma kusan Yarabawa miliyan 40 ne a yankin yammacin Afirka kuma da yawansu Yarabanci ne babban yarensu.

Daga cikin bukukuwan Isese da Yarabawa ke yi sun hada da bikin Eyo, Igogo, Ojude Oba, Olojo, Oro, da Sango.

Jihohi 4 sun ba da hutun bikin Isese

Bode Agoro, shugaban ma’aikata a Legas, ya ce matakin ba da hutun ranar Isese ya kara tabbatar da kudurin Babajide Sanwo-Olu na inganta al’adun gargajiya a jihar.

Sanarwar ta zo ne jim kadan bayan gwamnatin jihar Ogun ita ma ta ayyana ranar Talata a matsayin ranar da babu aiki domin gudanar da bukin a wani sako da ta wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

Garambawul: Gwamna ya rantsar da kwamishinoni 6, ya kirkiro sababbin ma'aikatu

Jaridar The Cable ta ruwaito gwamnatin jihar Osun, ta bakin kwamishinanta na harkokin cikin gida, Hon. Abdul-Rasheed Kayode Aderibigbe, ta ba ma'aikatan jihar hutun kwana daya.

"Muna sanar da jama'a cewa gwamnan Osun, Sanata Ademola Adeleke ya ayyana Talata, 20 ga Agustan 2024 a matsayin ranar hutu domin murnar "Ranar Isise."

- Inji sanarwar Hon. Aderibigbe.

Haka kuma gwamnatocin jihohin Oyo da Osun sun amince da ranar Talata a matsayin ranar hutu don bikin ranar Isese.

Bikin Isese na shekarar 2023

A wani labarin, mun ruwaito cewa, domin tunawa da ranar Isese ta 2023, akalla jihohi hudu a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya suka ba da hutun aiki ga ma’aikatan gwamnati.

An kebe ranar Isese a mafi yawan jihohin Kudu maso Yamma domin gudanar da bukukuwan al'adu na Yarabawa na asali da tushe da kuma kiyaye al'adun kabilar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.