Awori: Takaitaccen tarihin kabilar da ta fara zama a jihar Legas

Awori: Takaitaccen tarihin kabilar da ta fara zama a jihar Legas

- Tarihi ya bayyana yadda yarima Olofin da mabiyansa suka kwashe ya nasu ya nasu suka bar fadar sarki Oduduwa na Ile-Ife suka koma wurin rafin kudu

- Kamar yadda aka samu labari bayan kwanaki da ya bar Ile-Ife, kwanon kasa ya tashi ya koma kusa da Olokemeji wacce yanzu ake kira Abeokuta

- Bayan kwana 17 ya bar Abeokuta, inda wasu daga mabiya suka bishi yana yada zango yana tashi har sai da ya kai tsakiyar tekun Legas kafin ya nutse

Tarihi ya bayyana yadda yarima Olofin da mabiyansa suka bar fadar sarki Oduduwa dake Ile-Ife suka koma kusa da wani rafi dake bangaren kudu.

Olofin daya ne daga cikin 'ya'yan Oduduwa. Ance bayan kwanaki kadan da ya bar Ile-Ife, kwanon kasa ya tsaya kusa da Olokemeji kusa da Abeokutan yanzu. Bayan kwanaki 17, kwanon ya cigaba da tafiya, bayan kwana 17 ya kara tsayawa Oke-Ata.

Daga nan kwanon kasar ya cigaba da tafiya bai tsaya a ko ina ba sai kudancin wajen Abeokuta inda ya tsaya yayi kwana 17.

KU KARANTA: Matukin jirgi ya yi korafin matsala a injin sa'o'i kadan kafin ya rikito daga sama

Awori: Takaitaccen tarihin kabilar da ta fara zama a jihar Legas
Awori: Takaitaccen tarihin kabilar da ta fara zama a jihar Legas. Hoto daga Pulse.ng
Asali: UGC

A nan ne wasu mabiyan Olofin suka ya da zango suka cigaba da rayuwa. Wandannan mutanen ne wani mutum mai suna Aro-bi-ologbo-egan ya cigaba da mulkarsu.

Kwanon ya cigaba da tafiya ta rafi bai tsaya a ko ina ba a karo na hudu sai Isheri, inda ya dauki tsawon lokaci a nan.

Daga nan ne Olofin ya fara umartar mabiyabsa da su dinga yada zango a wurare na din-din-din bayan kwana 289 (17×17), lokacin kwanon ya kara tashi ya cigaba da tafiya.

Daga nan sai wasu mabiyan Olofin suka bishi, sauran kuma suna zaune wuri daya. Sun cigaba da tafiyar na kwana 2 lokacin da kwanon ya dan dakata a Iddo, jihar Legas.

Sai da ya kai Idumota dake tsakiyar Legas, inda ya nutse a tsakiyan ruwa bayan yin zagaye. Lokacin da Olofin ya koma Iddo don ya hadu da mabiyansa, sun tambaye shi inda kwanon yake, sai yace "Awo Ti Ri" ma'ana "Kwanon ya nutse". Daganan ne aka samu sunan Awori.

Awori yare ne a kabilar Yarabawa wadanda harshensu ya bambanta da asalin yaren Yarabanci. Yanzu haka ana samunsu a jihar Ogun da Legas dake Najeriya.

An yarda da cewa Awori daga bangaren Aworis suke, akwai musulmansu da kiristoci.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Akwai yuwuwar a sako 'yan bindiga da aka kama saboda yaran makarantan Kagara

A wani labari na daban, shagalin aure a kasar Sudan yana kwashe kwanaki da dama, inda ango da amarya suke taka rawa mabambanta.

Aure a Sudan yana da bangarori 3, sa ranar aure, shirye-shirye da kuma asalin shagalin bikin.

Sudan kasa ce wacce musulmai suka fi yawa, al'adu da shagulgulansu basu canza ba tsawon shekaru duk da dai akwai cigaba da aka samu na zamani.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng