Wasannin al’adun gargajiya: An farfaɗo da wasan Langa a jihar Kano (HOTUNA)

Wasannin al’adun gargajiya: An farfaɗo da wasan Langa a jihar Kano (HOTUNA)

- An gabatar da wasan Langa a tsakanin matasan jihar Kano

- Matasan sun ce sun yi wannan ne domin farfado da al'adun gargajiya na dauri

A ranar Lahadi 2 ga watan Yuli ne matasan jihar Kano suka farfado da dadaddiyar wasan gargajiya na kabilar Hausa mai suna Langa, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

An gudanar da wannan wasa ne a unguwar Zawaciki, inda aka fafata tsakanin yan Unguwar Makera Ja’en da yan unguwar Zawacikin.

KU KARANTA: Dansanda ya kiɗime, ya harbi kansa, yayi ƙoƙarin bindige kwamishinan Yansanda

Matasan sun bayyana farin cikinsu da gabatar da wannan wasa, inda suka ce manufarsu itace sada zamunta tare da maido da shaukin wasannin al’adun gargajiya tsakanin su.

Wasannin al’adun gargajiya: An farfaɗo da wasan Langa a jihar Kano (HOTUNA)
Wasan Langa

Ga wanda bai sani ba, ana gudanar da wasan langa ne tsakanin kungiyoyi guda biyu, inda ake tafiya akan kafa daya, tare da rike daya kafar da hannu guda daya, bayan an lankwasa ta, daga nan kuma sai a fara yar turereniya tsakanin kungiyoyin.

Wasannin al’adun gargajiya: An farfaɗo da wasan Langa a jihar Kano (HOTUNA)
Wasan Langa

Yadda ake gane zakara kuwa shine kungiyar da tafi kayar da yayan abokanan karawarta, kamar yadda majiyar Legit.ng ta bayyanan.

Wasannin al’adun gargajiya: An farfaɗo da wasan Langa a jihar Kano (HOTUNA)
Kungiyoyin da suka fafata

Sai dai a wannan zamani an fi samun almajirai a matsayin masu gudanar da wannan wasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin zaka baiwa Buhari kodar ka idan ya bukata?

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel