Ana sa ran Buhari Ya Koma Aso Rock, Tinubu Ya Kira Taron Majalisar Magabata na Kasa

Ana sa ran Buhari Ya Koma Aso Rock, Tinubu Ya Kira Taron Majalisar Magabata na Kasa

  • Shugaba Bola Tinubu zai jagoranci taron majalisar magabata na kasa a karon farko tun bayan hawwansa mulki watanni 14 baya
  • A yau Talata, 13 ga Agustan 2024 ne ake sa ran su Muhammadu Buhari, Olusegun Obasanjo, Abdussalam Abubakar za su hadu a Aso Rock
  • Majalisar magabata wata bangare ce ta gwamnatin tarayya da ke da alhakin ba bangaren zartarwa shawara kan tsara manufofi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A yau Talata ne ake sa ran dukkanin tsofaffin shuwagabannin kasa na farar hula da mulkin soja za su hallara a fadar Aso Rock Villa da ke Abuja.

Wannan na zuwa ne yayin da Shugaba Bola Tinubu ya kira taron majalisar magabata na kasa a karon farko tun bayan hawansa mulki watanni 14 baya.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Jigon PDP ya fadi yadda Tinubu zai magance matsalolin Najeriya

Tinubu ya kira taron majalisar magabata na kasa a yau Talata a Abuja
Tsofaffin shugabannin Najeriya za su gana a Abuja bayan Tinubu ya kira taron majalisar magabata. Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Bola Tinubu ya kira taron magabata

A taron na ranar Talata, jaridar The Punch ta ruwaito 'yan majalisar magabatan za su tattauna abubuwan da suka faru na baya-bayan nan a fadin kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kadan daga cikin abubuwan da suka faru sun hada da zanga-zangar yunwa da aka kammala ranar 10 ga Agusta, tattalin arziki da kuma matsalar tsaro.

Wata majiya ta bayyana cewa Shugaba Tinubu zai yi magana ne kan wasu muhimman abubuwa 7, yayin da ya yiwa taron take da: "Alakar zanga-zanga da tsaron kasa da kuma yanayin tattalin arziki."

Tambihi: Su wanene 'yan majalisar magabata?

Majalisar magabata wata bangare ce ta gwamnatin tarayya da ke da alhakin baiwa bangaren zartarwa shawara kan tsara manufofi.

'Yan majalisar sun hada da tsofaffin shugabannin kasa na farar hula da mulkin soja, tsofaffin alkalan alkalan Najeriya.

Kara karanta wannan

Yunwa na barazana ga rayukan almajiran Kano, an roki matasa su hakura da zanga zanga

Akwai kuma wadanda su ka rike kujerar shugaban majalisar dattawa a Najeriya.

Sauran 'yan majalisar sun hada da shugaban majalisar wakilai, gwamnoni, da babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), inji rahoton The Cable.

Ya taron majalisar magabata ke gudana?

Taron majalisar magabata dai yana gudana ne a zauren majalisar zartarwa na fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Shugaba mai ci ne ke jagorantar taron, tare da mataimakin shugaban kasa a matsayin mataimakin shugaban majalisar.

Taron na yau Talata na zuwa ne watanni 18 bayan da majalisar ta yi zamanta na karshe a Fabrairun 2023, a karkashin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Buhari ya kira taron majalisar magabata

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya kira taron majalisar magabata da masu ruwa da tsaki na kasa domin tattaunawa kan abubuwa biyu da suka shafi Najeriya.

An ce taron majalisar wanda ya gudana a ranar 10 ga watan Fabrairun 2023 ya duba abubuwan da suka shafi zaben shugaban kasa, yan majalisa da gwamnoni.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.